Minista Zai Taimaka Wa Gombe Shawo Kan Matsalolin Muhalli

Daga Khalid Idris Doya,

Ministan Muhalli, Dakta Mohammed Mahmood Abubakar ya bayyana cewa Jihar Gombe ta yi rawar gani a fannin kula da muhalli da hadin gwiwa da hukumomin gwamnatin tarayya da ke karkashin ma’aikatarsa.

Ministan ya bayyana shirin nan na ‘Gombe Koriya Shar wato 3G’ da Gwamna Inuwa Yahaya ya samar a matsayin jigo wajen kula da muhalli, kiyayewa da farfado da albarkatun kasa, yana mai kira ga sauran jihohin da ke fadin kasar nan su yi koyi da irin hakan.

Dakta Mahmood Abubakar ya bayyana hakan ne lokacin da Gwamna Inuwa Yahaya ya kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja, kamar yadda daraktan yada labaran gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya nakalto ta cikin wata sanarwar da ya rabar a jiya.

Ya lura cewa a yanzu Jihar ta Gombe ta yi suna a bangaren muhalli, sakamakon jajircewar gwamnatin jihar wajen magance kalubalen muhalli.

Ya ce, “Gombe ta yi nisa kuma ta aiwatar da abubuwa da dama a bangaren kula da muhalli. Don hakan ya dace da shirin ci gaban ku, na ga jerin ayyukan da kuke yi wadanda ke kara nuni da irin yadda kuka shirya kula da kuma alkinta muhalli.

“Babban abin da mutum zai iya yi yau a duniya don yaki da canjin yanayi shi ne dasa bishiyoyi da yawa kamar yadda kuke yi, ba za su yi yawa ba, bishiyoyi suna da alfanu matuka. A yau mun fi damuwa ne da zuke hayaki, bishiyoyi suna taka muhimmiyar rawa wajen zama wani bangare na tsarin tallafawa duniyar mu, matukar babu bishiyoyi abubuwa da dama zasu lalace.”

 

Ministan ya tabbatar wa Gwamna Inuwa Yahaya cewa Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya za ta ci gaba da yin aiki da Gwamnatin Jihar Gombe don magance duk matsalolin da ake da su, yana mai bayyana shirin da ma’aikatar sa ke yi na sake farfado da wuraren sarrafa shara a jihar don magance kalubalen kula da shara, inda ya ce tuni aka yi tanadin hakan a kasafin kudin bana ta wannan bangaren.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya tun da farko ya nemi karin tallafi daga gwamnatin tarayya don yaki da matsalar muhalli dake faruwa sanadiyyar kwarurruka fiye da 200 da ake dasu a fadin jihar.

Ya gode wa Ministan kan tallafin da Gombe ta samu ya zuwa yanzu daga ma’aikatar kula da muhalli, tare da neman karin hadin kai don Jihar da yankin Arewa Maso Gabas baki daya su ci gaba da amfana.

Gwamnan ya ce kasancewar jihar a yanki mai busasshiyar kasa da yanayin kasa maras karfi; Gombe tana fuskantar kalubale da dama na muhalli wadanda suka hada da ambaliyar ruwa, da sare dazuzzuka, da kwararowar hamada dama yawaitar kwarurruka.

Sai ya yaba da goyon bayan Ma’aikatar Kula da Muhalli ta Tarayya wajen tabbatar da fara aikin shawo kan matsalar zaizayar kasa ta Jami’ar Jihar Gombe dake gab da kammala, wadda ke gudana ta hannun hukumar NEWMAP.

 

“Game da sha’anin kwarurruka, na san cewa hukumar NEWMAP na gab da kawo karshe, kuma kamar yadda kuka ambata a baya, za a samu wani shirin da zai maye gurbin hukumar, don haka Jihar Gombe tana bukatar fifiko, saboda mun fara aiki kwanan nan, a cikin garin Gombe kadai akwai kwarurruka guda 5 da ake dasu wadanda suka kusan kilomita 30 kuma aikin kwarin da muke yi yanzu bai wuce tsawon kilomita 7 da rabi ba kawai.”

 

Yayin da yake bayyana kokarin da gwamnatinsa ke yi na sake farfado da muhalli, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce shirin na Gombe Koriya Shar wato 3G, ya shiga cikin shirin gandun daji na kasa wanda ke da aniyar shukawa da kula da bishiyoyi miliyan 25 a kowace shekara.

 

“Mun yi nasarar sanya jihar Gombe cikin jihohin dake kokarin tabbatar da dasawa da kuma farfado da kayan lambu ta yadda za a yi amfani dasu dangane don magance dumama da sauyin yanayi.”

 

Yahaya ya kuma nemi goyon bayan ma’aikatar don aiwatar da aikin hana zaizayar kasa a Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya FCE, wanda ya ce yana da matukar muhimmanci ga jihar da kuma samar da isassun kudade don ayyukan magance zaizayar kasa na Bogo da Dadinkowa don ba da damar kammala su akan lokaci.

 

A nasa jawabin, karamin Ministan Muhalli, Sharon Ikeazor, ya bayyana Jihar ta Gombe a matsayin kyakkyawar misali ga sauran jihohi, inda ya tabbatar wa Gwamna Inuwa Yahaya cewa ma’aikatar za ta hada kai da Gwamnatin Gombe don karfafa gwiwar matasan da ke da sha’awar shiga sana’ar bola jari don sake sarrafa robobi da karafa, yana mai cewa robobi ba illa kadai suke da shi ga muhalli ba, amma suna ma da hadari ga tsirrai da dabbobi.

Exit mobile version