Connect with us

LABARAI

Ministan Cikin Gida Ya Kaddamar Da Katafaren Ofishin NIS Na Jihar Kwara

Published

on

Ministan kula da harkokin cikin gida, Rauf Ogbeni Aregbesola ya kaddamar da babban ofishin Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) reshen Jihar Kwara a yau Talata 23 ga watan Yunin 2020, ta hanyar shafin intanet.

A yayin kaddamarwar, Ministan ya yi kiran kara nuna kishin kasa yayin gudanar da aiki a tsakanin jami’an hukumar ta NIS musamman wadanda suke kula da iyakokin kasa domin sauya kalmar da ake kwatanta iyakokin kasar nan da ita ta “mashigin kasa masu barayin hanyoyi”, wanda ya ce ya zama wajibi a sauya ta hanyar magance kumbiya-kumbiya da nuna rashin da’a a bakin aiki da kuma cin hanci bisa rungumar amfani da kyakkyawar manufar gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta fuskar tabbatar da kyakkyawan yanayi domin ‘yan kasuwa da masu zuba jari na kasashen waje su yi tururuwar zuwa Nijeriya.

Ministan ya tattauna da Gwamnan Jihar Kwara, Malam Abdulrahman Abdulrazak inda ya kaddamar da katafaren ginin ofishin NIS na jihar a madadinsa domin al’umma ta amfana.

A nata bangaren, babbar sakatariyar ma’aikatar harkokin cikin gida Barista Georgina Ekeoma Ehuriah ta taya Minista Aregbesola murnar zama shugaba mai albarka a ma’aikatar, kasancewar a lokacinsa ne aka kaddamar da galibin ayyukan ci gaba a karkashin hukumomin ma’aikatar.

Shi kuwa Shugaban NIS, CGI Muhammad Babandede yaba wa Minista Aregbesola ya yi bisa irin goyon baya da yake bai wa hukumar da kuma amincewa da bukatunta da ke bukatar sahalewar ofishinsa, inda hakan ya taimaka gaya wajen saukaka aiwatar da ayyukan ci gaba ire-iren wadannan da aka kaddamar a dan kankanen lokacin da ya kama aiki a matsayin ministan cikin gida.

               CGI Muhammad Babandede yana tsokaci a yayin qaddamar da ofishin na Kwara.

 

 
Advertisement

labarai