Ministan harkin cikin gida na Tarayyar Nijeriya Abdurra’uf Arebeosola ya nuna gamsuwarsa bisa yadda aikin ginin sabon Gidan gyaran halin da Gwamnatin Tarayya ke yi shiyyoyin kasarnan biyar harda Kano. Ministan ya bayyana haka ne alokacin ziyarar duba aikin ginin gidan Gyaran Halin da ake a Jihar Kano a ranar Asabar data Gabata.
Minista Abdurra’uf Arebeosola ya ce na gamsu kwarai da yadda aikin ke tafiya, musamman nagartasa da kuma yadda aka samar da ingantattun abububawan da ake bukata. Yace wannan na cikin kyawawan munufofin Gwamnatin Muhammadu Buhari na kyautata gidajen Gyaran Halin zuwa irin na zamani. Yace an tanadi dukkan abububawan da zasu taimaka wajen Inganta rayuwar mazauna gidan Gyaran Halin.
Ya ci gaba da cewa, dole ajinjinawa Gwamnatin Muhammadu Buhari bisa bujiro da sabbin tsare tsare da zasu kara Inganta rayuwar al’ummar kasarnan, saboda Haka sai ya bukaci jama’a da a cI gaba da yiwa Kasa addu’ar fatan dorewar zaman lafiya.
Shima da yake gabatar da jawabinsa shugaban Hukumar gidajen gyaran halin na Kasa Alhaji Ahmad Ja’afaru ya bayyana cewa muna farin ciki kwarai da ganin yadda Minista ya nuna farin cikinsa tare da gamsuwa da ingancin aikin da ake gudanarwa.
Tawagar Ministan ta hada da shugaban Hukumar lura da gidajen gyaran hali ta kasa Alhaji Ahmad Ja’afaru, Kwamandan Hukumar lura da gidajen gyaran hali na Jihar Kano, jami’an Hukumar tsaro ta cibil defence, Kwamandan Hukumar lura da shige da fice na Jihar Kano da sauran manyan baki.