Ministan harkokin wajen Nijeriya Mista Geoffrey Onyeama ya kamu da cutar korona. Ministan ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce an tabbatar da ya kamu da cutar bayan an yi masa gwajin cutar a karo na hudu.
A saƙon da ya wallafa, ministan ya ce a yanzu haka ya kama hanyar zuwa wurin killace masu ɗauke da cutar.