Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sanar a yau Jumma’a cewa, daga ranar 10 zuwa 12 ga watan Yuni, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, zai halarci taron ministoci masu bibiyar aiwatar da matakan da aka dauka na taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), gami da bikin bude baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da Afirka karo na hudu a birnin Changsha na lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)