CRI Hausa" />

Ministan Lafiyar Brazil: Ya Yiwu Yiwu Za A Fara Amfani Da Allurar Rigakafin COVID-19 Da Kasar Sin Ta Samar

Ministan kiwon lafiyar Brazil Eduardo Pazuello ya bayyana a kwanan baya cewa, kila za a fara amfani da alluran rigakafin cutar Covid-19 da kamfamin Sinovac na kasar Sin, da kamfanin AstraZeneca na kasar Birtaniya suka samar daga tsakiyar watan Fabrairun badi, ko da yake hakikanin lokacin da za a fara aikin ya dogara ga binciken hukumar sa ido.
An ba da labarin cewa, ministan ya halarci wani taron tattaunawa kan shirin amfani da allurar a wannan rana, bayan taron kuma ya nuna cewa, hukumar sa ido kan aikin kiwon lafiya ta kasar wato ANVISA, za ta yi nazari kan alkaluman gwajin allurar da ake yi a kasar a watan Jarairu mai zuwa.(Amina Xu)

Exit mobile version