Connect with us

LABARAI

Ministan Shari’a Ya Bukaci Buhari Ya Cire Magu

Published

on

A ci gaba da sa toka-sa-katsi da ake yi kan batun shugaban hukumar EFCC, Ministan Shari’a, kuma Antoni Janar na kasa, Abubakar Malami (SAN), ya aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasikar kar ta kwana kan shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu.
Malami ya bukaci shugaban kasan da ya tsige shugaban hukumar ta hana almundahanan bisa wasu zarge-zargen rashawa akalla 20. A cewar rahoton da jaridar Thisday ta fitar. Daga cikin zarge-zargen da Abubakar Malami ya yi wa Ibrahim Magu shi ne yana karkatar da kudaden sata kuma bashi da biyayya ga na gaba da shi a gwamnati.
Thisday ta samu labari daga majiyoyi daban jiya cewa Malami ya ba da jerin sunayen mutane uku da Buhari kan maye Ibrahim Magu da su.
Amma magoya bayan Magu dake cikin fadar shugaban kasa na cewa “Cire Magu a wannan lokaci da yake aiki tukuru na yaki da rashawa a gwamnatin Buhari na iya zama babban kuskure. Majiyoyin suka ce: “Abin takaici ne shugaban EFCC na fuskantar wasu miyagu da suka rantse sai sun cire shi duk da nasarorin da ya samu.” Amma fa sun ce duba ga irin tuhume-tuhumen da ake yi wa Magu, da yiwuwar Shugaban kasa zai bukaci nada kwamitin bincike kafin yanke shawara.
daya daga cikin majiyoyin ta ce: “Ina mai tabbatar muku cewa duk da cewa Magu ya tsallake ramukan muguntan da aka shirya masa a baya, na Antoni Janar din nan mafi karfin da ka iya tuge Magu daga EFCC saboda wasikar AGF na kunshe da tuhume-tuhume 22 masu nauyi da zai wajabtawa Buhari aika sunansa majalisa ko canza shi.”
Dalilin da ya sa hakan shi ne ma’aikatar Antoni Janar ke kula da hukumar EFCC saboda haka ba za’a yi watsi da shawararsa ba.” Wasu majiyoyin suka ce: “Malami na tuhumar Magu da girman kai da rashin biyayya gare shi a matsayin Minista mai kula da ma’aikatar EFCC.” Malami ya yi ikirain cewa Magu ya sayar da yawancin dukiyoyin da EFCC ta kwato ba tare da sanin kowa ba, kamar yadda majiyoyin suka kara.
Advertisement

labarai