Yusuf Shuaibu" />

Ministan Wasanni Ya Kaddamar Da Dakin Wasa A Dawakin-Kudu

Ministan wasanni da matasa Solomon Dalung, ya kaddamar da dan karamin filin wasa a Dawakin-Kudu da ke cikin Jihar Kano. Da yake jawabi wajen kaddamarwar a ranar Litinin, Dalung ya bayyana cewe, filin wasan zai bunkasa harkar wasanni a yankin.
A cewarsa, wannan aiki dai yana daya daga cikin manufofin shugaba Muhammadu Buhari, wajen kawo ci gaban matasa wadanda suka fi yawa a cikin al’umma. Ministan ya kara da cewa, gwamnatin Buhari na kokari wajen ci gaban matasa ta hanyar karfafa musu gwiwa wajen harkokinsu. Ya ce, filin wasan na Dawakin-Kudu yana daya daga cikin ayyukan da gwamnatin shugaba Buhari take gudanarwa a sassan kasar nan, domin ci gaban matasa wajen goyan bayan wannan gwamnati.
Ministan ya bayyana fatansa na yin amfani da wannan filin wasa a matsayin wajen motsa jikin matasa.
A cikin bayanin gwamna Abdullahi Ganduje, ya yaba wa gwamnatin tarayya na gina filin wasa a Kano. Ya bayyana cewa, wannan aiki ya nuna irin kokarin gwamnatin tarayya a kan ci gaban matasa. Ganduje ya shawarci matasan yankin da su yi amfani da filin wasan wajen karfafa wasanninsu. Ya ce, gwamnatin Jihar za ta kula da wannan filin wasa da kuma tabbatar da ganin an yi amfani da wurin yadda ya kamata.
Kamfanin dillanci labarai na kasa ta ruwaito cewa, a filin wasan har da filin wasa na kwallon kafa.

Exit mobile version