Aisha Alhassan ta mika wa fadar shugaban kasa takardar murabus din ta daga mukamin ministar harkokin mata bayan abinda ta kira rashin adalci da jam’iyyar APC mai mulki ta mata na rashin ba ta damar tsayawa takara ba tare da wani dalili da ya dace da doka ba.
Ministar ta bayyana yadda ta sanar da shugaban kasa anniyarta ta sake tsayawa takarar gwamna a zabukkan shekarar 2019, kuma har shugaban kasan ya nuna mata gamsuwar shi da hakan, amma abun mamaki sai ta ga sunan ta ba ya jerin sunayen wadanda jam’iyyar ta ba damar tsayawa takara, sannan babu wani dalili da aka bata na yin hakan.
Daga karshe ta bayyana cewa ta yi murabus daga mukamin ta na ministar harkokin mata.