Daga Nasir S. Gwangwazo,
Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta bayyana alhinin ta kan fadowar jirgin saman Rundunar Mayakan Sama ta Nijeriya (NAF) kirar Beechcraft KingAir B350i Aircraft a ranar Lahadi a Abuja.
Rahotanni sun ce jirgin ya samu matsalar inji bayan ya tashi sannan ya fado kasa.
Hajiya Sadiya ta bayyana bakin ciki kan hadarin jirgin da kuma asarar rayukan wadanda ke cikin jirgin da aka yi.
“Rundunar Mayakan Sama ta na bada matukar tallafi ga ayyukan mu na kai kayan agaji tun daga farkon kafa wannan Ma’aikata.
“Sun taimaka wajen daukar kayan agaji ga mutanen da wani abu ya faru gare su musamman a lokacin zaman tilas don rage yaduwar cutar korona a cikin shekarar 2020 da kuma zuwa ga wadanda annobar ambaliya da harin ‘yan bindiga da rikice-rikicen jama’a da sauran bala’o’i su ka shafa.
“Mu na godiya kan ayyukan ma’aikatan jiragen su, musamman matukan jiragen wadanda su ka shafe daruruwan awoyi su na tuka mu zuwa da dawowa ga yankunan da bala’o’i da sauran al’amuran jinkai su ka shafa.
“Mu na addu’ar Allah ya bada hakuri ga iyalan su da su ka bari a baya kuma ya ba su jimirin jure wannan rashi na masoyan su da su ka yi.”