Sagir Abubakar" />

Ministar Jinkai Ta Kaddamar Da Bada Tallafi A Jihar Katsina

Ministar Jinkai

Ministar kula da harkokin Jinkai, Agaji da kare Afkuwa Bala’o’i, Hajiya Sa’adiyya Umar Faruk, ta kaddamar da shirin bada tallafin kudade ga matan dake yankunan karkara a jahar Katsina.

Hajiya Sa’adiyya ta kaddamar da shirin ne a masaukin shugaban kasa na gidan gwamnatin Jahar Katsina.

Da ya ke jawabi a wajen taron gwamnati jihar Katsina, Aminu Bello Masari, wanda mataimakinsa, Alhaji Mannir Yakubu, ya wakilta ya bayyana jin dadinsa akan wadannan shirye-shirye da gwamnatin tarayya ke bullowa dasu domin bunkasa rayuwar al’umma a jahar Katsina da ma kasa baki daya.

Alhaji Mannir Yakubu yayi karin haske akan wasu shirye-shirye na gwamnatin tarayya wadanda a halin yanzu ke cigaba da gudana a jihar nan da kuma yadda suke haifar da kyakkyawan sakamako ga rayuwar wadanda ke amfana.

Kamar yadda ya ce shirye-shiryen sun hada da shirin bada tallafin kudade, da na ciyar da yara ’yan makaranta da makamantansu. Haka kuma, Ministar kula da harkokin jin kai ta kaddamar da shirin shiyyoyin dan majalissar dattawa na Katsina da Daura.

Ministar ta ce, za a bada tallafin Naira 20,000 ga mata marassa karfi ga mata 6,800 wadanda suka fito daga yankuna karkara a jihar Katsina. Hajiya Sa’adiyya faruk tace shirin nada nufin bunkasa rayuwar marassa karfi da gajiyayyu daga yankunan karkara.

Ministar tace gwamnatin tarayya ta kasha sama da Naira Miliyan dubu tara da Miliyan dari biyar ga magidanta sama da 443,000, karkashin shirin bada tallafin mai sharadi daga lokacin da gwamnatin APC ta dafa madafan iko zuwa yau. Hajiya Sa’adiyya ta hori al’ummomin da suka amfana da tallafin da aka basu wajen inganta kananan sana’o’insu.

Tun da farko maai bada shawara ta musamman akan bunkasa tattalin arziki da shirye-shirye Abdulkkadir Mamman Nasir yace an zabo wadanda zasu amfana ne daga cikin mata mafi bukatar taimako dake yankunan karkara a jahar nan.

Alhaji Abdulkadir Nasir ya bada tabbacin cewa wadanda suka amfana zasu yi kyakkyawan amfani daa tallafin bisa dalilan da suka sa aka ba su shi.

Exit mobile version