Ministar Mata Ta Sa Ana Mana Kallon Maciya Amana – Dalong

Da yake ga dukkanin alamu har yanzu kalaman da Ministar Mata, Hajiya Jummai Alhassan ta yi a kan goyon bayanta ga ubangidanta na siyasa, Alhaji Atiku Abubakar a zaben 2019 na cigaba da tayar da kura, Ministan Wasanni da Matasa, Barista Solomon Dalong ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi garambawul a majalisar ministocinsa.

A cewar Minista Dalong yin garambawul din ya zama wajibi saboda la’akari da wadanda suke neman cinna wa gwamnatin wuta kowa ya kone kurmus a siyasa.

Ya bayyana haka ne a wata zantawa da ya yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka a tsakiyar makon nan.

Ya ce, “Ba zai yiwu muna saida man fetur wani ya ce zai toya kosai a waje kusa da mu ba. Maganar da ta yi ta sa kowane Dan Nijeriya zai kalli mu ministocin Buhari a matsayin maciya amana. Da ta ajiye aikin nan sai ta yi abin da take so”.

Minista Dalong ya kara da cewa, abin da Minista Jummai Alhassan ta yi yunkuri ne na halaka mutanen da suke tafiya a jirgin ruwa a tsakiyar teku, “Ka ga idan ana cikin tafiya a jirgin ruwa a tsakiyar ruwa sai wani ya yi kokarin juyar da mutanen ciki a cikin ruwa, ai su mutanen cikin ba za su yarda ba. Sai a tsaya masa kawai shi da yake son halaka a ruwa ya sauka ko kuma na ciki su taru su jefa shi”, a ta bakin Ministan.

Ba wannan ne karon farko da wasu ke kiraye-kirayen shugaban kasan ya yi garambawul a majalisar zartaswarsa ba, domin ko a ‘yan makwannin da suka gabata, Kungiyar Kwadago a Kasa (NLC) ta nemi hakan har ma ta ce idan aka wuce wannan lokacin ba a yi ba, lokaci zai kure.

Exit mobile version