Jamil Gulma" />

Misali Daga Kebbi: Yadda Kananan Hukumomi Suka Shiga Uku A Nijeriya

Kamar dai yadda aka sani kananan hukumomi sune suka kasance mafi kusaci da talakawa, inda talaka ke tunanin samun sawaba a duk lokacin wata bukata ko matsi, musamman karamar bukata ko kuma ta gaggawa, amma a Nijeriya abin ya zamo akasin haka, inda yanzu haka akasarin ma’aikatun cibiyoyin kananan hukumomi suka koma kango sanadiyyar rashin zuwa aiki.

A Jihar Kebbi Wakilin LEADERSHIP A YAU ya zagaya wadansu kananan hukumomi, inda kuma ya zanta da wadansu mutane dangane da makomar kananan hukumomi a jihar.
Wani shugaban karamar hukumar mulki ya zanta da Wakilinmu kuma ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana masa da cewa, wallahi al’ummar yakin da ya fito ne suka yi tsaye akan sai ya yi wannan takarar, saboda kirkinsa, domin suna tunanin zai iya kawo gyara a cikin sha’anin mulkin karamar hukumar, amma sai bayan ya dare karagar mulkin ne sai ya tarar da abinda bai yi tsammani ba, saboda ba abinda ke ciki bayan rashin adalci da son rai daga sama, inji shi.
Ya kuma cigaba da cewa, wani lokacin sai ya ji kamar ya ajiye mulkin, to amma idan ya tuna da al’ummar dake bayansa, sai ya hakura bisa tunanin ko gaba wata dama zata iya fadowa, amma dai ya ce, ba zai sake shiga harkar siyasar ba daga yanzu.
Wadansu majiyoyi a Jihar Kebbi sun kuma labarta wa Wakilin na LEADERSHIP A YAU cewa, akwai wani shugaban karamar hukuma da ya yi kundumbala ya ajiye mulkin a sanadiyyar ba zai iya aikata kama-karya ba da yin yadda ake so ya yi da dukiyar al’umma ba daga sama a cikin gudanar da mulkinsa.
Majiyoyin har wa yau sun labarta wa Wakilinmu da cewa, sau da yawa za a sanar wa duniya cewa, an bai wa kananan hukumomi makuddan kudi, don aiwatar da wadansu ayyuka, inda kuma daga baya za a dawo cikin ruwan sanyi a janye, a bar musu wani kaso, wanda bai taka kara ya karya ba.
Alhaji Garba Salihu, wani tsohon ma’aikaci ne a karamar hukuma, wanda ya soma aiki a karamar hukuma tun tsohuwar Jihar Sokoto har zuwa lokacin da aka kirkiro Jihar Kebbi kuma har wa yau ya soma aikin ne a sashen kudi har zuwa matakin Shugaban Sashen (Director Finance and Supply), ya bayyana cewa, mutuwar kananan hukumomi ba shi da alaka da zaben wadanda ake so ko akasin haka; mutuwar kananan hukumomi ya samo asali ne tun da aka kirkiro asusun hadin gwiwa (Joint Account) a matakin jiha, wanda tun daga wannan lokacin aikin kananan hukumomi ya soma tabarbarewa, inda har ta kai ga babu wani aiki da ta ke iya aiwatarwa sai dai gwamnatin jiha, saboda ta hannun gwamnatin jihohi ne kudaden kananan hukumomi ke shigowa daga Gwamnatin Tarayya, wanda shine ya ba su damar yi wadaka da kudaden, illa sai abinda suka ga damar bai wa kananan hukumomi.
Sai ya ce, idan dai ana son gaskiya tare da taimaka wa talaka, to a bar wa kananan hukumomi kudadensu, domin sune suka fi kusanci da talakawa, kuma nan ne matsaloli suka fi kamari.
Yanzu haka dai don nemo bakin zaren warware matsaloli da kuma samun mafita  a kananan hukumomi da ma siyasar Jihar Kebbi musamman wajen zakulo mutanen kirki, don tsaya wa takarar mukaman siyasa daban-daban, wadansu manyan mutane da suka ajiye aiki, sun kutsa kai cikin siyasa, inda suka fantsama wajen neman gurabe a cikin wadanda ke da ruwa da tsaki wajen tsayar da ’yan takara (delegates).
Malam Musa Ibrahim, dan shekaru kimanin 65 kuma wanda ya ajiye aiki, ya bayyana abinda ya janyo hankalinsu har ya sa suka shiga siyasa tare da neman mukamai a jam’iyyu, inda ce duk wani bala’i da al’umma suka sami kawunansu a sanadiyyar wadannan deleget ne saboda su ke da hakki na tsayarda yantakara bisa ga sharadi na barazana daga gwamnati ko kuma sun karbi kudi daga hannun dantakara wadanda ba su taka kara suka karya ba ko da kuwa bai cancanta ba wanda za su iya kashe  wadannan kudaden cikin kasa ga mako daya amma sai su yi sanadiyyar shigar al’umma cikin bala’i a wani lokaci mai tsawo.
A sanadiyyar wannan al’umma musamman ma’aikatan da suka ajiye aiki da ma masu aikin gwamnati  sun dade suna shan wahala hannun yansiyasa inda mutum zai share shekaru yana aiki amma zama guda sai ka ga yansiyasa sun zo suna cin zarafinsu sannan kuma bayan  ajiye aiki hakkokansu su kasa fitowa sai an kai ruwa rana.

Exit mobile version