Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Mishkilar Lokutan Al’ada Da Daukar Ciki Ga Mata

by
3 years ago
in TASKIRA
4 min read
Daukar Ciki Bayan Shekara 35 Na Iya Haifar Da Matsaloli—Masana
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Ma fi yawan ‘yanmata ba su gane lokacin al’adarsu, saboda jinkunyar tambaya idan suka ga wani canji a jikinsu. ‘Yar’uwa, a duk lokacin da kika lura da samuwar wani canji a jikinki, abu na farko da za ki yi shi ne ki fara nazarin abin da ya haifar miki da wannan canji. Mai yiwuwa abu ne da ya shafi koshin lafiyarki, mai yiwuwa kuma abu ne da bashi da matsala wanda aka saba gani a wurin wasu da suka girme ki. Al’ada da daukar ciki abubuwa ne masu matukar muhimmanci ga rayuwar mata. Sai dai kuma a yawancin lokuta, mata musamman a kasarmu ta Hausa sukan rikice wajen iya rabe lokutan al’ada da kuma lokutan daukar ciki. Domin warware wannan rikicin, a karanta rubutun nan har karshe:

Lokacin Al’ada: Lokaci ne da jini ke fitowa ta al’aurarki wanda kike bukatar yin amfani da wani kyalle maitaushi don kada ya bata miki jiki.

Lokacin Da Jinin Ya Dauke: Kwanakin da jini ya dauke zuwa dawowar wani a wata. Misali, idan kika ga jini ran 11 ga Mayu, sai kuma kika sake gani ran 10 ga Yuni, to zai zama lokacin daukewar jininki shi ne kwana 30 watau, daga 11 ga Mayu zuwa 10 ga Yuni.

Labarai Masu Nasaba

Sirrukan Mata Da Galibin Maza Ba Su Sani Ba (I)

Alfanu Da Matsalolin Tiktok Ga Rayuwar Matasa

Ki Lura: Kada ki yi kuskuren cewa, kwana 28 ne kwanakin daukewar jininki, kowace mace na iya samun bambanci tsakaninta da wata na lokacin daukewar jini, wanda yakan kama daga kwana 21 zuwa kwana 35.

Lokacin Daukar Ciki: Wanna shi ne lokacin da mahaifa ta bude, kuma ana iya samun ciki a wannan lokaci cikin sauki. Lokacin kan fara daga mako 1 kafin fara al’ada. Ga hanya ma fi sauki da za ki lissa kwanakin daukar ciki.

1. Ranar da kika fara ganin jini.

2. Ki duba kwanan wata, sai ki kirga kwana 15 har da ranar farko.

3. Ki lura da ranar da kika fara kirgawa.

4. Ki yi wata alama, kwana uku kafin da kuma bayan wancan kwana 15.

6. In kika lura za ki ga kin yi alama a kwana 7.

Wannan kwana 7 su ne kwanakin da mahaifarki ta bude, saboda haka su ne kwanakin daukar ciki. Lokaci ne da idan aka sadu da mace kusan akwai tabbacin daukar ciki da kashi 98 daga cikin dari.

7. Ki yi wannan lissafin a kowane wata, idan kika cire wadannan kwanaki sauran kwanakin ba lallai ba ne in an sadu a dauki ciki. Misali,

1. Idan kin fara al’ada 11 ga Oktoban 2017,

2. Kwana 15 bayan fara al’adar zai zama 25 (har da ranar farko) ga watan Oktoban, mako 2 kenan bayan farawa.

3. Kwana 15 zai kama ranar 25 ga Agustan 2017 kenan.

4. Kwana 3 kafin ranar 25 su ne, 22 da 23 da 24.

5. Kwana 3 bayan 25 ga Agustan 2017 su ne, 26 da 27 da 28.

6.  Ranar 22 zuwa 28 ga watan watau kwana 7 kenan, su ne kwanakin da mahaifarki za ta bude. Kar ki manta wannan kwana 7 lokaci ne da maniyi ke zama a mahaifar mace.

Ida aka yi saduwa a cikin wadannan kwanaki, nan da nan maniyin ke fara zama wani sashi na halittar dan’adam. Haka kuma idan ana so a haifi mace, sai a yi kwanciyar auren a tsakanin kwana 3 kafin lokacin daukar ciki, watau ranakun 22, 23 da 24.

Idan kuwa namiji ake so mace ta haifa, sai a yi ibadar auren a lokacin daukar ciki ko kuma kwana 3 bayan ranar 25.

Alamomin Da Ke Nuna Kin Samu Ciki

Ko ba ki je wajen likita ba, za ki san cewa a mako 2 da daukar ciki za ki fara jin wadannan alamun:

1. Ciwon kai.

2. Zafin jiki.

3. Kasala da jin bacci.

4. Girman nononki zai karu kamar lokacin da kike al’ada.

5. Za ki kara sha’awa.

6.  Za ki ji kwibinki na yawan ciwo.

ADVERTISEMENT

7.  Za ki dinga jin zafin ciki.

8.  Saurin jin wari ko dandano ko gani sosai ko cin abinci da yawa.

9. Al’aurarki za ta yi fadi, in kika sa hannunki za ki ga wani fari-farin abu na fitowa.

Idan kika ji ciwon kai na damunki, sai ki koma ki duba lokacin al’adarki.

Ya kamata ki dinga shan maltina ko madara, kada kuma ki yi gaggawar zuwa kemis da zarar kin ji canji a jikinki, saboda za ki iya warwarewa cikin sauki, domin kuwa wani lokaci yawan shan kwayoyi na da hadari ko kuma ki sha fanadol kawai ya isa. 

Da fatan an amfana.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Kananan Hukumomi: Ciyamomi Kan Gaza Gane Jumlar Adadin Albashin Ma’aikatansu

Next Post

Manufar “Tsugunar Da Masu Fama Da Talauci A Wuraren Da Suka Dace” Ta Kyautata Rayuwar Iyalin Guan Ailing

Labarai Masu Nasaba

Sirrukan Mata Da Galibin Maza Ba Su Sani Ba (I)

Sirrukan Mata Da Galibin Maza Ba Su Sani Ba (I)

by Rabi’at Sidi B.
1 hour ago
0

...

Alfanu Da Matsalolin Tiktok Ga Rayuwar Matasa

Alfanu Da Matsalolin Tiktok Ga Rayuwar Matasa

by Rabi’at Sidi B.
7 days ago
0

...

Kwalliyar Sallar Da Ta Fi Birge Matasa A Wannan Shekarar

Kwalliyar Sallar Da Ta Fi Birge Matasa A Wannan Shekarar

by Rabi’at Sidi B.
2 weeks ago
0

...

Sallah

Tsokaci Game Da Sabon Salon Da Za A Ci Bikin Sallah Da Shi Bana

by Rabi’at Sidi B.
3 weeks ago
0

...

Next Post

Manufar “Tsugunar Da Masu Fama Da Talauci A Wuraren Da Suka Dace” Ta Kyautata Rayuwar Iyalin Guan Ailing

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: