Kayan Hadi
1-Albasa
2-Tumaturin gwangwani
4-Mai
5-Sinadarin dandano
6-Gishiri
7-Kayan Kamshi
Yadda A Ke Hadawa
Uwargida da zarar kin tanadi kayan hadin imiyar ki, sai ki wanke Naman ki, ki yanka Albasa ki sa gishiri da kayan kamshi ki zuba a cikin Naman sai ki dora a wuta, ki barshi ya dahu sosai ya yi Lugub sai ki sauke. Sai ki sami Albasarki mai yawa ki yanka su Dede gwargwado. Ki wanke ki tsabtace ta. Sai ki zuba mangyada a wuta. In ya yi sai ta zuba Albasar nan mai yawa ki rage wuta ki barta ta yi ta dahuwa kina yi kin juyawa, a haka had ta narke. Sai ki dauko Tumaturin Kwangwanin ki Dan damashi da ruwa sai ki zuba a cikin Albasar ki kara soyasu. Sai ki dauko ruwan naman da naman gaba daya ki juye a cikin miyar. Kada a zuba ruwan da yawa saboda ba a son ruwa ya yi yawa. Don itama Albasar ruwace. Sai kisa sinadarin girkin ki da gisiri ki kara kayan kamshi kadan ki bar miyar ta dahu ta hada jikinta sosai. Sai ki sauke. Za a iya ci da shinkafa ko kuskus ko taliya makaroni, doya da sauran su.