Daga Bilkisu Tijjani Kassim,
Abubuwan Da Uwargida Yakamata Ta Tanada:
Yalo, Tattasai, Tumatur, Albasa, Manja, Alaiyahu, Gishiri, magi, kuri, kifi banda.
Yadda ake hada miyar yalo
Da farko za ki fara gyara kayan miyarki sai ki jajjaga su kamar yadda za ki yi kowace miya sannan ki yayyanka Albasarki a tsattsaye, sa iki samu tukunya ki fara zuba Manjan a ciki, idan ya yi zafi sa iki zuba Albasa a ciki, sannan ki zuba jajjageggen tumatur da tattasan ki soya su daga nan iki zuba kifinki a ciki amma kar ki babbare shi haka za ki sa shi daya dayansa, sai ki juya su gaba daya, sannan ki zuba yalonki amma za ki yayyanka shi ne, sannan ki zuba magi da gishiri da kuri, daga nan ki mammotsa shi wato ki jijjuya shi ko ina, sannan ki kawo alayyahu wanda dama kin yayyanka shi ki zuba ki jujjuya shi sannan ki kawo ruwanki dan kadan ki zuba yadda de zata yi dan ruwa-ruwa haka saboda ba’a so ta yi kauri tafi dadi haka, sai ki jijjuya shi sannan ki rufe ki barta ta danyi kamar minti 15 zuwa 20.
Za ki ga yadda za ta yi kyau ta yi kuma dandano. Ita wannan miya ana ci da shinkafa da Tuwon shinkafa da tuwon semo ko teba ko doya ko sakwara, sannan za ki iya ci ma da sufa geti duk abin da kika samu za ki iya ci da shi ita ana cin kome da ita.