Connect with us

KASASHEN WAJE

Mnangagwa Ya Dauki Rantsuwar Kama Aiki A Matsayin Shugaban Zimbabwe

Published

on

Ya dauki rantsuwar kama aiki ne a yau Lahadi a gaban dubban ‘yan kallo a filin wasa a babban birnin kasar Harare.
Lokaci ya yi da yakamata mu hada kai mu tafi tare, inji Mnangagwa mai shekaru 75 a wurin bukin rantsar da shi.
Zaben da Mnangagwa ya lashe a wata da ya gabata, shi ne na farko a cikin shekaru da dama da aka yi ba tare da dadden shuagaban kasar Robert Mugabe a ciki ba, kuma madugun ‘yan adawan kasar Nelson Chamisa shi ne dan takarar babban jami’iyar adawa ta Mobement for Democratic Change a zaben.
Mnangagwa ya samu kashi 50.8 cikin dari na kuru’un, amma kotu ta dakatar da rantsar da shi saboda wata kara dake gabanta. Shiko shugaban ‘yan adawa Chamisa da ya samu kasha 44 cikin dari, yace shi ne ya lashe zaben.
A shekaranjiya Juama’a ne kotu ta amince da nasarar da Mnangagwa ya yi da karamin rata.
Advertisement

labarai