MO IBRAHIM 2017

Bishir Dauda 08165270879

Shugabanci nagari har yanzu shi ne matsalar da kasashen Afirka da dama ke fafutukar samu tun bayan kawo karshen mulkin mallaka. Duk wani taro, walau taron lacca ne ko na kara ma juna sani, za ka samu ana tattauna kalubale da kai tsaye suna da alaka da shugabanci . Wannan dalilin ya sa masana da masu sharhi da dama kan nahiyarmu ta Afirka ke ta’allaka matsalolin nahiyar da rashin shugabanci nagari.

Kazalika wannan dalilin dai shi ne ya jawo hankalin duniya  ga nahiyar inda ake ta shigo da abubuwa daban-daban da za su kawo ma Afirka shugabanci nagari.

A yayin da  Amerika da kasashen yammacin turai ke maida hankalin wurin bada tallafi da zai kara zaunar da Dimokaradiyya daram a nahiyar, akwai kuma gidauniyoyi daban-daban da an kafa su ne kacokan domin su karfafa shugabanci nagari ta hanyoyi daban-daban. Wadansu daga cikin irin ire-iren wadannan gidauniyoyi, kasashen waje ne kamar Amurka, Japan,Birtaniya, Jamus, Faransa da sauran su ke tafiyar da su. Akwai kungiyoyi dake aikin yaki da cin hanci da rashawa kamar Transparency International, da kungiyoyi dake aikin kare hakkin bil’adama kamar Amnesty International, da masu aikin sanya ido game da zabe da tattalin arziki kamar Plan Internation da dimbin su ga su nan, duk dai dodo daya suke ma tsafi, wato yaya za a samu shugabanci nagari a nahiyarmu ta Afrika.

Daya daga cikin gidauniyoyi da ‘yan asalin nahiyar suka kafa kacokan don karfafa shugabanci nagari a kasashen Afirka  ita ce gidauniyar MO Ibrahim wadda fittaccen attajirin nan dan asalin kasar Sudan Mohammed  Ibrahim ya kafa kuma yake assasawa domin samar da kyakkyawan jagoranci a kasashen Afrika.Tun kafa wannan gidauniya mutum hudu (4) ne suka taba lashe kyautar  wadanda dukkaninsu tsofaffin shugaban kasashe ne, dama kuma kyautar an yi ta ne don shugabannin kasashen Afirka wadanda suka taka rawar a zo a gani. Wadannan shugabanni sun hada da Joakuim Chissano na Mozambikue wanda ya lashe kyautar a shekarar 2007, sai Festus Mogae na Botswana 2008,Pedro Pires,na Cape Berde a 2011  Hifikepunye Pohamba na Namibia, 2014 .  2015 da 2016 ba a samu shugaban kasa daya daga cikin kasashe 54 na nahiyar Afirka da ya iya lashe wannan gaggarumin tukici sai yanzu da

a karo  na biyar aka samu wata zakakura shugaba da ta lashe wannan kasaitaciyyar kyauta  wannan ba kowa ba ce, face tsohuwar shugabar kasar Liberia, Ellen Jhonson Sirleaf.

A ta bakin shugaban kwamitin bada kyautar, Salim Ahmed Salim,  ya  fadi dalilin da yasa suka zabi  Ellen Jhonson Sirleaf. Ya ce , “Ellen Jhonson Sirleaf  ta karbi shugabancin kasar Liberia a lokacin da yakin basasa yai rugu-rugu da  kasar,sannan ta jagoranci yin sulhu da yaimaida hankali kacokan kan  gina kasar da cibiyoyin dimokaradiyya .A wa’adi biyu da tai, ta yi aiki tukuru a madadin mutanen Liberia, kana ta fuskanci kalubale daban-daban. Duk da haka mulkin Ellen Jhonson Sirleaf na shekaru 12 ya kafa damba wadda za a dasa don gina kasar Liberia”.

Hakika kowa ya ci zomo, kamar yadda masu iya Magana ke cewa ya ci gudu. Ba haka kawai kwamitin bada kyautar Mo Ibrahim ya zabi Ellen ya bata wannan kyautar alfarma ba. Domin wannan kwamitin yana da wasu ka’idoji da yake bi wajen tantance shugaban da ya cancanci amsar wannan kyauta. Wadannan ka’idoji ana kiran su da turanci “ Ibrahim Inded of African Gobernance” sun hada da:

Rukunnai hudu :Kiyaye doka da oda,kare hakkin dan adam da tafiyar da mutane a sha’anin mulki,samar da damarmaki da suka shafi arzikin kasa ga mutane,gina al’umma. A karkashin kowane rukunni akwai abubuwa da dama kamar kare rayuka da dukokiyoyin al’umma, gaskiya da tsare dukiyar al’umma,rage wariyar jinsi,samar da kayayyakin more rayuwa, inganta karkara,inganta ilimi, fannin lafiya da sauran su.

Idan muka nazarci tarihin siyasar kasar Liberia, wanda ke cike da abin ban takaici kama daga asalin yadda aka kafa kasar ta hanyar tsugunnar da bayin da aka kwato daga hannun masu safarar su zuwa Turai da Amurka, zuwa yake-yaken basasa da kasar ta tsunduma daga baya-baya, za mu ga cewa lalle Ellen Jhonson Sirleaf ta cancanci a yaba mata, kuma ta ci a kira ta mace wadda tafi ma mazan, domin za mu ga rawar da shugabanni maza suka taka wajen lalata kasar Liberia, abin sai dai a Lahira kawai Allah yai sakayya wa bayinsa.

Ellen ta zabi tai rayuwa abin  misali, ba tare da amubazzaranci da dukiyar kasarta ba. Ta ki ta bi son zuciyarta, ta azurta kanta da dukiyar baitul mali, alhali dimbin talakawan kasarta, na fama da matsalar abinci, rashin aikin yi da batun rashin ingantaccen kiwon lafiya. Har Allah yasa ta kamala mulkinta lafiya ba a same ta da halin bera ba, kuma gwamnatinta ba a samu badakalar cin hanci da rashawa  da yawa  ba. Wani abin burgewa ga shugabancin Sirleaf shi ne yadda ta hada kai da sauran shugabannin kasashen Afirka, domin aiki tare don a shawo maganin wasu muhimman matsalolin dake fuskantar nahiyar. Hakika mun ga irin kyakkyawan shugabancinta a kungiyar ECOWAS da kuma hadin kai da taba kungiyar hadin kan Afirka ta AU da sauran kungiyoyin ci gabannahiyar Afirka.Babban gudunmuwarta shi ne samar da zaman lafiya,wannan bai yiwuya idan babu adalci da shugabanci nagari.

Da Ellen taso da sai tai katsi-landan a al’amurran hukumar zaben kasar Liberia, ta tabbatar jamiyyarta ce ta lashe zaben da akai kwanan nan, to amma maimakon tai abinda aka saba gani a kasashen Afirka da dama, sai tai abin da ba a saba gani ba.Kai  Idan ma fa, ta ga dama zata iya canza kundin tsarin mulkin Liberiadomin ta tabbata kan mulkin Liberia  kamar yadda akai a wasu kasashen irin su Janhoriyar Dimokaradiyyar  Kongo,Burundi da sauran su, ta jefa miliyoyin mutane cikin ukuba da masifar yaki. Duk Ellen batai haka ba, sai tai abinda ya dace, ta nuna halin dattijantaka wadda a yau tai karanci a mafi rinjayen kasashen Afirka.

Za mu ce nasarar da Ellen Jhonson Sirleaf ta samu ta lashe wannan gaggarumar kyauta, nasara ce ga bakidayan talakawan Afirka wadanda shekara da shekaru ake wasan kwallo da su. Aka hana su shugabanci nagari, abinda yasa nahiyar ta kasance cikin yunwa, fatara, cututtuka, mutane basu iya cin lafiyayyen abinci, ba wurin kwana, babu kyakkyawan ilimi. Ga matasa nan sai mutuwa sukea banza  akan hanyar su ta ketarawa zuwa tsibirin Lampedusa.

Muna fatan sauran kasashen Afirka suma za sui hobbasa wajen samar da shugabanci nagari a kasashen su ko tarihi yai masu kyakkyawan muhalli.

Ga Abin da Ellen Jhonson  Sirleaf  ta ce  a lokacin da aka sanar da ita cewa ita ta lashe kyautar Mo Ibrahim ta shekarar 2017:

“Ba karamar karramawa ba ce a ce gidauniyar Ibrahim ta ba mutum wannan kyauta. Na zabi in yi aiki tukuru da bauta ma mutanen Liberia, kuma ina godiya gare su akan wannan dama da suka ba ni.

A matsayina na mace ta farko da ta karbi wannan kyauta, ina fatan hakan ya karfafa ma mata da ‘yan mata guiwa, su kawar da duk wasu kalubale da shamakai da suke fuskanta domin su cimma mafarkinsu. Duk inda ke akwai na daya, to za a samu na biyu, na uku dama na hudu.

Ina godiya cewa gidauniyar MO Ibrahim ta ba ni wannan girmamawa bisa yadda na karfafa dimokaradiyya a mulkina na wa’adi biyu. Hakika babban alfaharina shi ne, yau bayan shekaru 30 na yaki a Liberia, iko yakoma hannun inda yakamata ya kasance wato a wurin jama’a, bisa doka da oda , da kuma hukumomi masu karfi. Kuma ina alfahari da cewa  Liberia ita ce kasa  daya a nahiyar da ta samu kyautatuwar dukkanin rukkunan mizanin kyakkyawan shugabanci da gidauniyar Mo Ibrahim ke amfani das u.Wannan kyakkyawar shaida ce ga daukacin wadanda sukai aiki a gwamnatina.

Gidauniyar Mo Ibrahim zata ci gaba da zama mai tasiri wajen ci gaban nahiyarmu. Sun riga sun sanza alkiblar shugabanci, wannan shi ne batun da zan ci gaba da yadawa bayan da na kamala wa’adin shugabancina”.

 

Exit mobile version