Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce yawan albarkatun gona da Sin ke shigowa da su daga kasashen Afirka na kara fadada, inda a watannin 11 na farkon shekarar 2020 da ta gabata, adadin ya karu da kaso 4.4 bisa dari, wanda kuma hakan ya nuna dorewar wannan ci gaba cikin shekaru 4 a jere.
Da yake karin haske game da hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis, kakakin ma’aikatar cinikayyar Gao Feng, ya ce cikin watannin 11, jimillar kudaden cinikayyar sassan biyu ta kai dalar Amurka biliyan 167.8.
Gao ya ce kasar Sin ce babbar abokiyar huldar cinikayyar nahiyar Afirka cikin shekaru 11 a jere, inda ta zamo ta biyu wajen shigo da albarkatun gona daga nahiyar.
Kaza lika jami’in ya ce, Sin ta tallafawa nahiyar a fannin gina layukan dogo da manyan titunan mota da suka kai tsawon sama da kilomita 6,000, da kuma kusan tashoshin ruwa 20, da sama da manyan ayyukan samar da lantarki 80. Sauran sun hada da sama da cibiyoyin kiwon lafiya 130, da filayen wasa 45 da kuma makarantu 170.
A daya hannun kuma, kamfanonin Sin sun samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 4.5 a kasashen nahiyar. Kaza lika Sin za ta ci gaba da karfafa tushen hadin gwiwar ta da kasashen Afirka, da marawa ci gaban nahiyar baya, tare da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga kowa karkashin hadin gwiwa da kasashen nahiyar ta Afirka. (Mai fassara: Saminu)