Moctar Ouane Ya Zama Sabon Firaministan Kasar Mali

An sanar da nada sabon Firaiminista a kasar Mali, matakin da zai kai ga janye wa kasar jerin takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba mata bayan juyin mulkin a watan da ya gabata.

Kafar talabijin din kasar ta sanar da cewa sabon shugaban riko na kasar, Bah Ndaw ya nada Moctar Ouane a matsayin Firaminista wanda tsohon ministan harakokin wajen Mali ne tsakanin shekarar 2004 zuwa 2011.

Exit mobile version