Modibbo Kilo: Gwarzuwarmu Ta Mako

Modibbo Kilo (1901-1976): Rayuwarta Da Ayyukanta Na Adabi

An ce Modibbo Kilo muzakkarar mace ce kamila mai kwarjini da haiba ga mutane. An yi bayanin shakkar ta da kwarjinita  ga mutane. Duk wanda ya tunkare ta tilas ya shiga taitayinsa wanda bai da nutsuwa ba ya iya tunkararta. Mace ce mai  kwarjini inda maza da mata ke shakkarta , wanda ba shi da imani ba zai iya tunkararta ba.

 

Nasabarta

Modibbo Kilo diya ce ga Alkali Mahamud dan Muhammadu Ashuru dan Sheikh Muhamud Hafiz dan Musa Hafiz dan Abubakar Amiru Barambo. Mahaifin Modibbo Kilo Alkali Muhamudu Filato Borno ne , wanda ya taso daga Kukawa ta kasar Misau cikin kasar Borno ya yi hijira zuwa kasar Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo. Mahaifin Kakanta dan’uwa ne ga gwani Mukhtar wanda ya karbi tuta a hannun mujaddi Shehu Usmanu Danfodiyo kuma ‘ya’yansa da jikokinsa su ne suke sarautar sarkin Misau.

A lokacin da mahaifinta ya zo Sokoto sai aka yankar masa fili a garken Nana Asama’u aka yankar masa wurin zama a shiyyar Gidadawa.

 

Haihuwarta

An haifi Modibbo Kilo a wajejen 1901 a garin Sokoto a shiyyar Gidadawa a unguwar Takardawa ( Bayan gidan Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto). Sunanta na gaskiya Saudatu amma an fi saninta da Kilo wanda ta sami wannan lakanin ne saboda a lokacin haihuwarta sarkin musulmi Abdurrahman dan Atiku ya nada mahaifinta a Alkali.

 

Tashinta da Karatunta

Tunda Modibbo Kilo ta tashi ba ta san komai ba sai dai karatu.Ta fara karatu a hannun mahaifinta Alkali Muhammadu kuma gare shi ta yi saukar alkur’ani tun tana ‘yar shekara Bakwai.  Ta yi tishin karatun wajen malamarta Modibbo Fadimatu sannan ta ci gaba da karantar da ita littattafan sani irin su, Usuliiddini da ahlari da ishmawi da  da Iziyya da Risala da Kurdabi da lawwali da sani da kuma tafsiri. Ta ci gaba da karatu a hannun yayanta Malam Shehu muhutin Sakoto da mijinta sarkin yamman Kware Abdullahi Bayero wanda shi ya dau ragamar koyar da ita bayan ya aure ta.Sannan ta yi karatu a hannun malamarta Modibbo Hauwa’u Mammange ta sauke ishiriniya a hannun yayanta Shehu Muhuti.

Modibbo Kilo ta mayar da karatu babbar sana’arta da za ja same ta tana yi dare da rana kullum ka ganta da littafi a hannunta ko dai tana karatu ko tana karantarwa. Modibbo Kilo ba ta zuwa ko’ina in ba da larura ba mace ce mai yawan sallah da tasbihi sannan da sauran ibadu.

Aurenta

An yi wa Modibbo Kilo aure tana ‘yar shekara tara. Ta auri sarkin yamman Kware Abdullahi Bayaro dan malam Isa autan Shehu Usmanau Danfodiyo tana da abokan zama guda biyu. A hannun mijinta ne ta sami ilimi mai yawan gaske har ta kai tana koyarwa  a cikin gidansa sun zauna lafiya da mijinta duk da dai daga baya sun rabu. An ce dalilin rabuwarsu shisshigi ta yi masa a wata fatwa da aka zo masa da ita bayan ya amsa sai ta yi masa gyara . Ta kuma wani auren inda ta auri Malam Akwara malami ne kuma dan kasuwa amma shi ma auren ya mutu a dalilin karatu inda ta daga murya a wani lokaci da take yin karatu aka ce shi kuma ransa bai so hakan ba. Bayan ya sake ta ba ta kara wani aure ba har ta koma ga mahaliccinta. Modibbo Kilo ba ta taba haihuwa ba. Tta rasu a garin Makka a shekarar 1976.

 

Ayyukanta na Tafsiri da Adabi

Modibbo Kili ta yi dimbin ayyuka duk da dai wasu ayyukan ba su zo hannu ba amma ta yi ayyuka sosai a  Sokoto da Makka musamman bangaren karantarwa da kuma rubce-rubuce sai dai da yaw aba su samu a hannu baa amma ga kadan da suka zo hannu.

Ta fara koyarwa a gidan Mahaifinta a unguwar Takardawa a lokacin da ta koma gidanta da ta gada nan ma ta ci gaba da koyarwa a Shazalawa ta mayar da makarantar ta can. Ta kuma karantarwa a hubbaren Shehu Usman Danfodiyo Ta loyar da dimbin maza da mata musamman ‘yan’uwanta haka tana amsa fatawa . Gidanta kullum a cike yake mata da maza Ta zama malamar tafsiri amma kafin ta fara a makarantarta sai da ta fara ja wa Modibbo Hauwa baki tukunna.

Kamar yadda Modibbo Kilo ta yi bayani a wakarta ta hijira ta nuna ta yi hijira ne zuwa Makka  saboda wasu abubuwa da ta gani na gurbacewar al’umma da kuma abubuwa da take ji a jikinta da zuciyarta na shaukin saduwa da Annabi Muhammadu SAW . Sarkin Musulmi Abubaka Na uku shi ya ba ta cikakken goyon baya har ya ba ta guziri na fam goma ya sa aka yi mata fasfo sannan ya tura ta wajen sarkin Kano don ya hada ta da ayari wato abokan tafiya.

A makka nan ma aikin Modibbo Kilo shi ne koyarwa gidanta wanda yake unguwar Jawal wanda yake dutse cikin Hara el Yamen ko da yaushe gidanta a cike yake da dalibai. Tana karatar da su fikhu da Hadisi.Tana  tafsiri ga mata ta hanyar amfani da tafsiril jalalaini musamman lokacin azimi.

A bangaren rubutattun wakoki kuwa Modibbo Kilo ta yi wakoki da dama duk ta yi su ne da ajami. Daga cikin wakokin akwai:-

 

Wakar Hijira

Wannan wakar ta yi ta ne kan hijirar da ta yi daga Sokoto zuwa Makka a cikin waakar ta fadi dalilin da ya sa ta yi hijira. Ciki da nuna hijirarta umarni ne ta samu daga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Sallahu alaihi wassalam inda take ceewa :-

Ni dai Rasulu llahi yac ce Saudatu

Taso fito maza zo cikin Haramaini.

A cikin wakar ta yi bayani dalla-dalla tun daga fitowarta daga gida Sokoto har zuwanta Kano har isarsu Makka. Wakar na da baiti 555.

Wakar Alkur’ani

Wakar Kabli da Ba’adi

Wakar Nasiha ga gabobi bakwai

Wakar taya murna ga Alkali Umaru

Wakar Burin Modibbo Kilo zuwa Makka

Wakar Hikaya

Wakar Hatsin bara

A bangaren rubutun zube Modibbo Kilo ta yi rubututtuka da daman gaske ciki akwai :-

Labarin manzancin Annabi Muhammadu Da halifancinsa sahabbai da mulkin Usmaniyya.

Farkon al’amarin Mujaddadi Nuruz zamani

Labarin sarkin musulmi Muhammadu Bello

Labarin Abubakar Atiki shakikin Muhammad Bello

Labarin Sarautar Aliyu Dan Muhammadu Bello

Labarin Sarautar Ahmadu Dan Atiku

Labarin sarautar Aliyu Karami Dan Muhammad Bello

Labarin Sarautar Ahmadur Rufa’I Dan Mujaddadi Usmanu

Labarin Sarautar Abubakar Atiku Karami Dan Mai Raba.

Labarin Sarautar Mu’azu Dan Muhammadu Bello

Labarin Sarautar Umaru Dan Aliyu

Labarin Sarautar Abdu Dan Atiku Dan Mujaddadi Usmanu

Labarin Sarautar Attahiru  Dan Amadu

Labarin Sarautar Muahammadu Dan Ahmadu

Labarin Sarautar Muhammadu dan Muhammadu

Labarin Sarautar Hasan Dan Mu’azu

Labarin Sarautar Abubakar Dan Usmau

Labarin ‘yanuwan Mujaddadi Shehu Usmanu

Labarin matan Shehu Usmanu

Labarin ‘ya’yan Shehu Maza da mata.

Labarin ‘ya’yan Muhammad Bello

Labarin Abdullahi Bin Fodiyo

Labarin ‘ya’yan Abdullahi Bin Fodiyo

Da sauransu.

Daga cikin daliban Modibbo Kilo na Sokoto Akwai:-

Alkali Mamman dan yayanta  da Alkali isah da malam Garba da iyalan wazirin Sokoto da na waziri Abbas da modibbo Khadijatu.

A makka kuwa Modibbo Kilo tana da dalibai kamar haka:-

Ta karantar da babban malamin nan na Sokoto Sheikh Sidi Attahiru da Khadi Usman Gusau da sheikh Halliru Binji shi ma ya zama khadi a jahar Sokoto dda Sheikh Abdurrahman Usmanu Magribi da sauransu. Allah ya jikan Modibbo Kilo Amin

 

Mun ciro wannan tarihin daga littafin  Modibbo Kilo (1901-1976)  Rayuwarta Da Ayyukanta (Ta Biyu Ga Nana Asama’u Bin Fodiyo A Karni Na Ishirin), wanda  Sa’adiyya Omar ta wallafa. Mun sami littafin ta hannun Alhaji Yusuf Dingyadi. Duka Allah ya saka musu da alheri. Amin.

Exit mobile version