Abba Ibrahim Wada" />

Modric Ya Ce Ba Zai Ba Ni Riga Mai Lamba Goma Ba – Eden Hazard

Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Edin Hazard, ya bayyana cewa zuwansa kungiyar bazai fara kishi da kowa ba saboda haka bazai damu da daukar bugun fanareti ba ko kuma lamba mai kyau sai dai zai mayar da hankali wajen ganin kwallonsa tayi kyau domin taimakawa kungiyar.

Hazard ya bayyana hakane bayan da Real Madrid ta gabatar dashi a gaban magoya bayanta ranar Alhamis bayan da Madrid din ta dauko Hazard daga Chelsea kan yarjejeniyar shekara biyar, kan kudi da ake cewa zai kai fam miliyan 150.

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Belgium ya koma Chelsea daga kungiyar kwallon kafa ta Lille dake kasar Faransa a shekara ta 2012, ya kuma bar chelsea ne bayan da ya lashe manyan kofuna shida da buga wasa 352 ya kuma ci kwallaye 352.

“Na yi Magana da Modric ta hanyar dan wasa Kobacic ko zai bar min riga mai lamba goma idan na koma Real Madrid amma sai yace bazai barmin ba kuma yace kawai inje in nemi wata lambar” in ji Modrid (Yana Dariya)

Ya ci gaba da cewa “Riga mai lamba 10 ba itace a gabana ba babban abinda yake gabana shine saka rigar wannan kungiyar mai tarihi kuma in buga wasa mai kyau kuma hakan nake fata saboda haka bazan shiga sahun masu buga bugun fanareti ba saboda akwai masu bugawa da dama wadanda nazo na samesu suna dauka”

A kakar wasan data gabata dai dan wasan baya Sergio Ramos ne ya buga fanareti takwas cikin 12 da kungiyar ta samu sai Karim Benzema wanda ya dauki guda uku sai kuma dan wasa Gareth Bale wanda ya buga guda daya.

Exit mobile version