Modric Ya Sake Lashe Babbar Kyauta

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Luka Modric ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kudu maso yammacin Turai na shekarar 2018, wato Balkan Athlete of the year.

Modric dan asalin kasar Croatia shi ne dan kwallon kafa na biyu da ya ci kyautar, bayan Hristo Stoichkob gwarzon dan kwallon kafar nahiyar Turai a shekarar 1994 sai kuma wannan lokacin daya lashe kyautar.

Dan wasan mai shekara 33 ya yi nasara ne da maki 77 a biki na 46 da kamfanin yada labarai na Bulgaria (BTA) kan gudanar, ya kuma doke Nobak Djokobic, dan wasan Tennis, wanda ya jera karo biyar yana lashe kyautar tun daga shekara ta 2011 zuwa 2015.

“Nayi farin ciki da lashe wannan lyautar saboda duk lokacin da wani ya lashe wata kyauta tabbas dagewa da jajircewa ce tasa hakan kuma ina fatan nan gab azan sake samun damar lashewa” in ji Modric, wanda tsohon dan wasan Tottenham ne

Yaci gaba da cewa “Bazan taba mantawa da ‘yan uwana ‘yan wasan kasar Crotia bad a kuma na kungiya ta ta Real Madrid wadanda suke taimakamin koda yaushe wajen ganin nasamu nasara a kowanne wasa”

Modric shi ne ya lashe kyautar Ballon d’Or ya kuma ci kofin Zakarun Turai da na Zakarun nahiyoyin duniya da Real Madrid, ya kuma kai Croatia wasan karshe a kofin duniya shi ne gwarzon gasar a Rasha.

Exit mobile version