Abba Ibrahim Wada" />

Modric Zai Sake Sabon Kwantaragi Da Real Madrid

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Luca Modric, zai sake sabon kwantaragi da kungiyar na tsawon shekara biyu kamar yadda kungiyar ta bayyana a shafinta na yanar gizo.
Modric, wanda shine gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya na hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ya shafe shekara da shekaru a Real Madrid sai dai a kwanakin baya an bayyana cewa dan wasan ya so komawa kungiyar Inter Milan ta kasar Italiya.
Sake sabon kwantaragin zai sanya kungiyar Inter Millan ta hakura da nemansa bayan da a watannin baya kungiyar ta bayyana aniyarta ta siyan dan wasan dan asalin kasar Crotia da haihuwa.
Dan wasan yakoma Real Madrid ne a shekara ta 2012 daga kungiyar kwallon kafa ta Tottenham akan kudi fam miliyan 33 kuma tun bayan komawarsa kungiyar ta Real Madrid ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin zakarun turai guda hudu.
Rahotanni sun bayyana cewa wakilin dan wasan da kungiyar Real Madrid sun cimma yarjejeniya akan sabon kwantaragin da dan wasan zai kara kuma nan gaba kadan kungiyar zata sanar a hukumance.
Real Madrid dai tana mataki na uku akan teburin laliga yayinda Barcelona da Atletico Madrid suke zaune a gabanta sai dai har yanzu kungiyar tana fafatawa a gasar cin kofin zakarun turai inda ta buga wasan farko da kungiyar Ajad ta kasar Holland.

Exit mobile version