Akwai yiwuwar ɗan wasan gaba na Chelsea Alvaro Morata zai yi jinyar sama da wata guda bayan raunin da ya samu a yayin fafatawar da suka sha kashi a hannun Manchester City a ranar Asabar.
Morata mai shekaru 24 ya koma Chelsea ne daga Real Madrid akan farashin Pam miliyan 60, kuma shi ne ɗan wasan da ya fi ci wa Chelsea ƙwallaye a wannan kaka, in da ya zura ƙwallaye bakwai.
Kazalika ɗan wasan ba zai samu damar buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ba da ƙasarsa ta Spain za ta yi da Albania da Isra’ila a wannan mako.