A jiya Talata, kasar Morocco ta karbi kaso na biyu na alluran rigakafin cutar COVID-19 da kamfanin Sinopharm na kasar Sin ya samar, ma’aikatar lafiyar kasar ce ta bayyana hakan.
A cewar ma’aikatar lafiyar, alluran rigakafin kimanin 500,000 daga kasar Sin sun isa filin jirgin saman Mohammed V dake Casablanca, da safiyar ranar Talatar, daga bisani kuma za a rarraba su zuwa cibiyoyin rigakafin da aka tanada a duk fadin kasar ta arewacin Afrika.
Morocco ta fara yin rigakafin a kasar a ranar 28 ga watan Janairu, bayan isar kashin farko na alluran rigakafin COVID-19 daga kasar Sin.
Ya zuwa ranar Litinin din da ta gabata, an yiwa mutane 1,707,091 rigakafin annobar COVID-19 a kasar Morocco. (Mai fassarawa: Ahmad daga CRI Hausa)