Yusuf Shuaibu" />

Mota ta Murkushe Dan Sanda Mai Ba Da Hannu A Legas

‘Yan sanda sun cafke wani direba mai suna Abuchi Okpara bisa zargisa da murkushe dan sanda mai ba da hannu mai suna Ogunmeru Obafemi a karamar hukumar Igando cikin Jihar Legas. Okpara ya gudu zuwa kasar Ghana bayan faruwar lamarin, an dai cafke shi ne ta hannun maigidansa shugaban kamfanin sufuri ta King Solomon Chariots mai suna Johnson Ogbonnaya.
A bayanin wani jami’i na ranar Talata mai suna Mahmud Hassan ya ce, Okpara ya gudu Ghana ne saboda ya gudumma abin da ake zargisa da shi domin kada ya fiskanci shari’a.
Okpara ya murkushe Obafemi ranar Talata da ta gabata a lokacin da yake kokarin kubuta daga kamun da aka yi masa sakamakon karya dokar hanya da ya yi.
“Shi dai direban da ake zargi yana jigila ne tsakanin Ghana da Nijeriya da mota mai lamba kamar haka KJA 633 DT, ya sauke fasinjojin ne a ina baikamata ba a Igando.
“Direban ya ki bin umurnin Ogunmeru dalilin da suka sa ya kama shi, Okpara a kokarisa na gudu da matarsa sai ya murkushe wannan jami’in,” inji Hassan.
Majiyarmu ta labarta mana cewa an garzaya da jami’in babban asibitin dake Igando sannan daga bisani aka kai shi asibitin koyarwa ta Jihar Legas dake Ikeja.
Hassan ya ce, an gurfanar da direban a kotu dake Igando kuma ma har an yanke masa hukuncin zaman gidan yari a Kirikiri.

Exit mobile version