Ahmed Muhammad Danasabe" />

Motar Tanka Ta Yi Sanadin Rasuwar Mutum 30 A Kogi

Akalla mutane talatin ne suka rasa rayukansu inda yawancinsu suka kone kurmus babu kyaun gani a  yayin da kuma da dama suka samu munanan raunuka a sakamakon fashewar wata tankar dakon man fetur wacce ta kama da wuta a unguwar Felele da ke yankin birnin Lokoja a jiya Laraba.

Ganau wadanda lamarin ya faru a idonsu, sun shaida wa manema labarai cewa hadarin ya auku ne da misalin karfe 8.30 na safe.
Sun ce akasarin wadanda lamarin ya rutsa da su yara kanana ne yan makarantun firamare da sakandire wadanda tun da sanyin safiya suka fito suna jiran a daidaita sahu don kwashe su zuwa makarantunsu.
Wadanda lamarin ya faru a idon na su sun kuma shaida cewa akwai daliban kwalejin kimiya da fasaha ta jihar Kogi( Kogi Poly)  da matafiya da kuma masu sana’oi  cikin wadanda hadarin ya rutsa da su.
Kamar yadda suka ce, lamarin ya auku ne a yayin da birki ta tsinkewa direban motar tankar tun daga kauyen Cruisher da ke kan babban hanyar Okene zuwa Lokoja, kafin ya kai unguwar Felele inda motar da fadi a GT Filaza wanda matattare ne na jama’a. Faduwar motar ke da wuya,sai kawai ta kama da wuta inda nan take motoci da a daidata sahu da ke harabar filazan su ma suka kama da wutar,lamarin da ta yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla talatin wanda a kasarin  kananan yara yan makaranta lamarin tafi shafa.
Jami’an hukumar kiyaye hadura ta kasa( FRSC) sun kwashi gawarwakin mutunen da suka rasa rayukansu zuwa asibintin kwararru na jihar Kogi da ke garin Lokoja, inda suka a jiye su a dakin ajiye gawarwaki,a yayin da kuma wadanda suka jikata suna kwance a asibitoci dabam dabam na jihar don karban magani.
Hanyar ta felele dai tana daya daga cikin hanya da ke cin rayukar jama’a a jihar Kogi idan aka yi la’akari da yawan hadaruruka da suke aukuwa a kowa ce shekara a kan babban hanyar.
Ko a ranan lahadi data gabata,sai da mutune da dama suka rasa rayukansu a kauyen Akpogu da ke yankin Koton karfe a jihar Kogi sakamakon fashewar tankar mai.

Exit mobile version