Abba Ibrahim Wada" />

Mourinho Na Fatan A Sayo Masa Bale A Tottenham

Sabon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Jose Mourinho, yana fatan kungiyar ta sayo masa tsohon dan wasan ta, Gareth Bale, domin yana ganin zai taimaka masa wajen farfado da martabar kungiyar a halin yanzu.
Bayan da kungiyar ta maye gurbin Mauricio Pochettino da Mourinho a ranar Laraba, kungiyar tayi alkawarin zata bashi makudan kudade domin sayan sababbin ‘yan wasan da zaiyi aiki dasu a kakar wasa mai zuwa.
Sai dai kamar yadda rahotanni daga kasar Ingila suka bayyana, Mourinho yana ganin kwarewar dan wasa Bale da kuma yanayin kasancewarsa tsohon dan wasan kungiyar zai sanya yaji yana bukatar sake komawa.
Bale dai ya kasance dan wasan da Tottenham baza ta manta dashi ba saboda irin kokarin da yayi a lokacin da yake buga mata wasa mafin kuma daga baya ya koma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a shekara ta 2013.
Mourinho dai zaiyi amfani da rashin jituwar da take tsakanin Bale da kociyan kungiyar, Zinadine Zidane wajen jan hankalin dan wasan ya amince ya koma kuma tuni suka shirya fara yiwa dan wasan Magana a watan Janairu mai zuwa.
A kwanakin baya Bale ya kusa komawa wata kungiya a kasar China da buga wasa kafin daga baya Real Madrida taki amincewa da cinikin kuma a halin yanzu yana da ragowar kwantiragin shekara biyu da rabi tare dasu.

Exit mobile version