Mourinho Ya Caccaki Alkalin Wasa

Mourinho

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Jose Mourinho ya caccaki alkalin wasa Andre Mariner bayan kungiyar sa ta yi rashin nasara a gida a hannun Chelsea wadda ke ci gaba da samun nasara a karkashin kocinta, Thomas Tuchel, yayin da ta dare mataki na 6 a teburin gasar firimiyar Ingila.

Chelsea ta doke Tottenham ne da ci daya mai ban haushi a bugun fanariti ta hannun Jorginho tun kafin tafiya hutun rabin lokaci wanda kuma da wannan kwallon aka karkare wasan babu wata kungiya data sake zura kwallo a raga.

Chelsea ta samu fanaritin ne sakamakon ketar da Eric Dier ya yi wa Timo Werner a da’irar mai tsaron raga, amma Mourinho wanda ya dauki tsawon lokaci yana yarfa wa alkalin wasan magana, ya ce, yana daukar sa a matsayin daya daga cikin kwararrun alkalan firimiyar Ingila, amma kuma ya ba shi kunya.

Mourinho ya ce, bai kamata alkalin wasan ya bai wa Chelsea bugun fanaritin ba saboda abune wanda dole sai ‘yan wasan baya sunyi kuma idan har za’a ci gaba da bayar da irin wannan bugun fanaretin tabbas za’a bata kwallon kafar Ingila.

Exit mobile version