Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester united, jose mourinho yace bazai iya bawa dan wasan gaba na kungiyar Rumelu Lukaku hutu ba saboda har sai ibrahimobic yadawo daga jiyya.
Ya bayyana hakane a jiya a yayin hirarsa da manema labarai a shirye shiryen kungiyar na buga wasa da Crystal Palace a satin wasa na 7 a filin wasa na old Trafford.
Mourinho yace lukaku ne kadai dan wasan da zai buga masa abinda yakeso saboda Marcos Rashford da Anthony Martial yana amfani dasu a wani wajen daban saboda haka bazai dinga yawan canja musu waje ba.
Yace idan har zai bawa lukaku hutu to dole sai idan har zlatan ibrahimobic yadawo daga jiyya sannan zai iya ajiye lukaku ya huta.
Lukaku dai yaci kwallaye goma tun bayan daya koma Manchester united daga Everton a cikin watan yulin daya gabata akan kudi fam miliyan 75.