Abba Ibrahim Wada" />

Mourinho Ya Mayar Da Tottenham Babbar Kungiya – Klopp

Mourinho

LONDON, ENGLAND - JANUARY 22: Jose Mourinho, Head Coach of Tottenham Hotspur talks to his players in the tunnel at half time during the Premier League match between Tottenham Hotspur and Norwich City at Tottenham Hotspur Stadium on January 22, 2020 in London, United Kingdom. (Photo by Tottenham Hotspur FC/Tottenham Hotspur FC via Getty Images)

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Kloop, ya ce, ya yi matukar mamakin yadda Jose Mourinho ya mayar da kungiyar Tottenham tamkar inji mai bada sakamako nan take.

Wannan na zuwa ne a yayin da yaran Kloop masu rike da kambun gasar ta firimiya suka hadu da Tottenham wadda ke jan ragamar gasar firimiyar Ingila a jiya Laraba kuma Kloop ya ce, yanayin yadda Tottenham ke doka wasa a wannan shekara na da kayatarwa.

Ana iya cewa Mourinho ya yi kokarin farfado da martabar Tottenham lura da cewa, lokacin da ya karbi ragamarta, tana can mataki na 14 a teburin firimiya fiye da shekara guda da ya gabata kuma wannan ba karamar bajinta bace.

Yanzu an wayi gari kungiyar na jan ragamar teburin gasar ta firimiya, yayin da Liverpool ke biye da ita a matsayi na biyu kuma ranar Laraba Liverpool ta karbi bakuncin Tottenhma a wasan mako na 13 a gasar Premier League da suka kara a filin wasa na Anfield.

 

Yadda kungiyoyin suka kara a tsakaninsu a baya:

Wasa daya Liverpool ta yi rashin nasara daga wasanni 15 a gasar Premier League haduwar baya-bayan nan da Tottenham ta ci 10 da canjaras hudu kuma cikin wasanni 26 a baya da Tottenham ta ziyarci Anfield a Premier League sau daya ta doke Liverpool shi ne cikin watan Mayun shekara ta 2011.

Tottenham ta yi rashin nasara a wasa biyar a jere da Liverpool a dukkan fafatawa da suka yi, idan aka sake doke ta zai zama karon farko ta sha kashi sau shida a jere kuma wannan mummunan tarihi a wajen kungiyar wadda take jin yanzu karfinta ya kawo.

 

Kwazon da Liverpool ke yi:

Liverpool ta barar da maki 11 da ya kamata ta samu a kakar bana, bayan buga wasanni 12 sai dai  a bara sai da tayi fafatawa 35 da ta kai yin asarar maki 11 wanda hakan yasa wasu suke ganin abune mai wahala kungiyar ta iya lashe gasar firimiyar bana.

Kungiyar ta Anfield ta lashe dukkan wasanni shida da ta yi a filin wasa na Anfield a bana da cin kwallaye 18 aka zura mata shida a raga sannan dan wasa Mohamed Salah ya ci kwallo 10 a gasar Premier League ta bana

Har yanzu ba a doke Liverpool a wasan gida ba a Premier League tun rashin nasara a hannun Crystal Palace da ci 2-1 a watan Afirilun shekara ta 2017 kuma kungiyar ta buga wasanni 65 kenan da cin 54 da canjaras guda 11.

Liverpool ta yi nasara a wasanni 10 a gida a Premier League a fafatawa da wadanda suke shidan farko a kan teburin Premier League bugu da kari kungiyar Anfield ita ce kadai ta zura kwallo a kowanne wasan Premier League da ta kara a bana.

Sadio Mane ya yi wasa bakwai bai ci kwallo ba a gasar Premier League a bana, kuma karon farko da ya dade bai zura kwallo ba a raga tun da ya koma Liverpool duk da cewa yana buga wasa duk sati.

Liverpool ta yi nasarar cin fenareti guda 18 a gasar Premier League da take samu sai dai za’a iya cewa kungiyar kwallon kafa ta  Sunderland ce ta ci fenareti 23 a jere a gasar tsakanin Maris din 2021 zuwa Janairun 2017.

 

Kokarin da Tottenham ke yi:

Tottenham ta ci wasanni bakwai a Premier League da canjaras hudu, tun bayan rashin nasara a wasan farko a kakar bana a hannun Eberton wadda da farko ta fara kokari kafin daga baya karsashin ‘yan wasan kungiyar ya dusashe.

Ba a doke Tottenham a wasan waje shida da ta buga ba, ta yi nasara a hudu da canjaras biyu kuma Tottenham ta hada maki 70 a karkashin Jose Mourinho tun da ya koma kungiyar sai kungiyar Manchester City tana da 75 sai Liverpool mai maki 90 sune ke gabansa.

Mourinho bai yi nasara a kan mai koyarwa Jurgen Klopp a wasa biyar a waje da suka fafata a dukkan karawa ba sai adai duk da haka ya yi canjaras a wasanni biyu da rashin nasara a wasanni uku.

Wannan shi ne wasan waje da ya buga da yawa da bai samu sakamako ba a jere tun lokacin da ya zama kocin kwallon kafa idan aka hada kokarinsa a kungiyoyin FC Porto da Chelsea da Inter Milan da Real Madrid da Manchester United.

Harry Kane da Son Heung-min sun ci kwallo 12 a tsakaninsu a bana a gasar Premier League, kuma saura kwallo daya su yi kan-kan-kan da tarihin da Alan Shearer da Chris Sutton suka kafa a gasar firimiyar a shekarar 1994 zuwa 1995.

A kwallaye 24 da Tottenham ta zura a raga a bana, Son ya ci 10 sai Harry Kane mai guda tara sannan Kane din ya ci kwallo a wasa hudu baya da ya buga a filin wasa na Anfield, amma a karawar an yi canjaras biyu da shi da rashin nasara biyu a kwallayen da ya zura a raga.

 

Exit mobile version