Abba Ibrahim Wada" />

Mourinho Ya Soki Real Madrid A Kan Rashin Nasara A Hannun Barcelona

Tsohon mai horar da kungiyar Manchester United Jose Maourinho, ya zargi Real Madrid da gazawa wajen nuna kwazon da ake bukata, a wasan El Clàsico da suka fafata da Barcelona a ranar Asabar, 2 ga watan nan na Maris.
Mourinho, wanda ya taba horar da Real Madrid a shekarun baya, ya bayyana rashin jin dadin yadda wasannin tsakanin tsohuwar kungiyar tasa da Barcelona ya kaya, inda Reala Madrid din ta sha kashi har sau biyu a haduwar da suka yi cikin kwanaki hudu
Kungiyoyin sun soma haduwa a wasan kusa da na karshe na gasar Copa del Rey inda Barcelona ta lallasa Real Madrid da kwallaye 3-0, sai kuma wasan La Liga da Barcelona ta yi tattaki har zuwa fillin wasa na Santiago Bernabeau ta samu nasara kan Real Madrid da 1-0.
Karo na farko kenan cikin shekaru 87, da Barcelona ta shiga gaban Real Madrid a jimillar wasannin da suka fafata da samun nasara kan juna, inda a yanzu kididdigar ta nuna cewa, Barcelona ta lallasa Madrid sau 96, yayinda ita kuma Real Madrid ta samu nasara kanta sau 95.
Haka zalika karo na farko kenan cikin shekaru 15, da Real Madrid ke shan kaye a hannun Barcelona har gida sau uku a jere idan aka hada da wasan da suka fafata a kakar wasan data gabata a wasan zagaye na biyu.
Mourinho, wanda karo na farko kenan yayi magana kan halin da Real Madrid ta shiga na fuskantar kalubalen rashin nasarori, ya ce kungiyar ta rasa kwarjinin da ta shahara da shi a baya kuma yakamata suyi kokarin shawo bakin zaren.
Jose Mourinho, na daga cikin masu horarwar da ake sa ran za su iya maye gurbin kocin Real Madrid na yanzu Santiago Solari kuma ya koyar da Real Madrid ne daga shekara ta 2010 zuwa ta 2013.

Exit mobile version