Abba Ibrahim Wada" />

Mourinho Ya Yi Korafi A Kan Fifita Wasu Masu Koyarwa

Mourinho

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Jose Mourinho, ya ce bai ga abin daga hankali ba kan ikirarin da Liverpool ke yi na yawan ‘yan wasan ta da ke ci gaba da jinya, gabanin haduwarsu ta ranar Laraba karkashin gasar Firimiyar Ingila.

A cewar Mourinho dan wasa daya kacal ne ya san cewa yana jinya a Liberpool, kuma dama kowacce kungiya tana da nata irin wannan matsaloli sai dai yadda Liberpool take zuzuta ciwon ‘yan wasan nata abin mamaki ne da abin kunya, in ji Mourinho.

A hirarsa da manema labarai bayan wasan da kungiyarsa ta sha kashi daci 2-1, Mourinho ya ce Birgil ban Dijk ne kawai dan wasan Liberpool da ya san yana jinya kuma ko da aka tambayi Mourinho kan raunin James Milner sai ya kada baki ya ce Tottenham za ta yi wasan ne ba tare da Erik Lamela ba wanda shima ke jinya.

Kafin wasan wanda aka buga a filin wasa na Anfield Tottenham din ce dai ke saman teburin Firimiya amma maki daya da Liberpool face banbancin yawan kwallaye sai dai yanzu Liberpool ta koma ta daya da tazarar maki uku a tsaaninsu.

 

Baya ga Ban Dijk din da James Milner Liberpool ta yi wasan ne ba tare da zaratan ‘yan wasanta irinsu Joe Gomez, Diogo Jota, Kostas Tsimikas, Thiago Alcantara da Dherdan Shakiri, Naby Keita da Joel Matip ba wadanda duka suke jinya.

Wasan dai na ranar Laraba shi ne ya fayyace kungiyar da za ta ci gaba da jagorancin teburin na Firimiya tsakanin Liberpool da Tottenham gabanin tafiya hutun karshen shekara wanda ake shirin tafiya nan gaba kadan.

Bayan tashi daga wasan ne Mourinho ya bayyana cewa halayyar da Jurgen Klopp na Liberpool ya nuna a filin wasan idan shi ne da tuni an koreshi daga cikin filin kuma sai dakatar dashi ko kuma aci tararsa ta kudi inda yace ana fifita wasu masu koyarwar akan wasu.

Yadda kungiyoyin suka kara a tsakaninsu a baya

Wasa daya Liberpool ta yi rashin nasara daga wasanni 15 a gasar Premier League haduwar baya-bayan nan da Tottenham ta ci 10 da canjaras hudu kuma cikin wasanni 26 a baya da Tottenham ta ziyarci Anfield a Premier League sau daya ta doke Liberpool shi ne cikin watan Mayun shekara ta 2011.

Tottenham ta yi rashin nasara a wasa biyar a jere da Liberpool a dukkan fafatawa da suka yi, idan aka sake doke ta zai zama karon farko ta sha kashi sau shida a jere kuma wannan mummunan tarihi a wajen kungiyar wadda take jin yanzu karfinta ya kawo.

Kwazon da Liberpool ke yi

Liberpool ta barar da maki 11 da ya kamata ta samu a kakar bana, bayan buga wasanni 12 sai dai  a bara sai da tayi fafatawa 35 da ta kai yin asarar maki 11 wanda hakan yasa wasu suke ganin abune mai wahala kungiyar ta iya lashe gasar firimiyar bana.

Kungiyar ta Anfield ta lashe dukkan wasanni shida da ta yi a filin wasa na Anfield a bana da cin kwallaye 18 aka zura mata shida a raga sannan dan wasa Mohamed Salah ya ci kwallo 10 a gasar Premier League ta bana

Har yanzu ba a doke Liberpool a wasan gida ba a Premier League tun rashin nasara a hannun Crystal Palace da ci 2-1 a watan Afirilun shekara ta 2017 kuma kungiyar ta buga wasanni 65 kenan da cin 54 da canjaras guda 11.

Liberpool ta yi nasara a wasanni 10 a gida a Premier League a fafatawa da wadanda suke shidan farko a kan teburin Premier League bugu da kari kungiyar Anfield ita ce kadai ta zura kwallo a kowanne wasan Premier League da ta kara a bana.

Sadio Mane ya yi wasa bakwai bai ci kwallo ba a gasar Premier League a bana, kuma karon farko da ya dade bai zura kwallo ba a raga tun da ya koma Liberpool duk da cewa yana buga wasa duk sati.

 

Liberpool ta yi nasarar cin fenareti guda 18 a gasar Premier League da take samu sai dai za’a iya cewa kungiyar kwallon kafa ta  Sunderland ce ta ci fenareti 23 a jere a gasar tsakanin Maris din 2021 zuwa Janairun 2017.

Kokarin da Tottenham ke yi

Tottenham ta ci wasanni bakwai a Premier League da canjaras hudu, tun bayan rashin nasara a wasan farko a kakar bana a hannun Eberton wadda da farko ta fara kokari kafin daga baya karsashin ‘yan wasan kungiyar ya dusashe.

Ba a doke Tottenham a wasan waje shida da ta buga ba, ta yi nasara a hudu da canjaras biyu kuma Tottenham ta hada maki 70 a karkashin Jose Mourinho tun da ya koma kungiyar sai kungiyar Manchester City tana da 75 sai Liberpool mai maki 90 sune ke gabansa.

Mourinho bai yi nasara a kan mai koyarwa Jurgen Klopp a wasa biyar a waje da suka fafata a dukkan karawa ba sai adai duk da haka ya yi canjaras a wasanni biyu da rashin nasara a wasanni uku.

Wannan shi ne wasan waje da ya buga da yawa da bai samu sakamako ba a jere tun lokacin da ya zama kocin kwallon kafa idan aka hada kokarinsa a kungiyoyin FC Porto da Chelsea da Inter Milan da Real Madrid da Manchester United.

Harry Kane da Son Heung-min sun ci kwallo 12 a tsakaninsu a bana a gasar Premier League, kuma saura kwallo daya su yi kan-kan-kan da tarihin da Alan Shearer da Chris Sutton suka kafa a gasar firimiyar a shekarar 1994 zuwa 1995.

A kwallaye 24 da Tottenham ta zura a raga a bana, Son ya ci 10 sai Harry Kane mai guda tara sannan Kane din ya ci kwallo a wasa hudu baya da ya buga a filin wasa na Anfield, amma a karawar an yi canjaras biyu da shi da rashin nasara biyu a kwallayen da ya zura a raga.

 

Exit mobile version