Mourinho Yana Son Siyan Isco

Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tashiga zawarcin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Isco domin yakoma kungiyar a karshen kakar nan da ake bugawa.

Dan wasan mai shekara 22 a duniya yakoma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ne daga kungiyar Malaga dake kasar sipaniya inda kuma yabuga wasanni da dama a kungiyar sannan kuma ya wakilci kasar sa ta sipaniya a wasanni da dama da kungiyar ta buga.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ce dai take zawarcin dan wasan bayan da mai koyar da yan wasan kungiyar Pep Guardiola ya bayyana Isco a matsayin wanda zai maye masa gurbin Dabid Silba wanda shima dan kasar sipaniya ne.

Sai dai mai koyar da kungiyar Manchester United yafara zawarcin dan wasan wanda shima yake ganin zai maye masa gurbin Machael Carrick wanda shima zaiyi ritaya a karshen kakar nan.

A kwanakin baya dai mai horar da yan wasan na Manchester United ya bayyana cewa yanason siyan yan wasan tsakiya guda biyu wadanda zasu maye masa gurbin Machael Carrick da Maroune Fellaini wadanda duk ake rade-radin zasu bar kungiyar a karshen kaka.

Isco dai yafara wasanni 14 ne kacal a kungiyar a wannan kakar biyu daga ciki kuma tun farkon watan Janairun daya gabata.

Exit mobile version