Moyes Da Van Gaal Basu Tabukawa United Komai Ba — Mourinho

Mai horar da Manchester United Jose Mourinho, ya ce kungiyar ta gaza kare martabar kwarewar da aka santa a kai, a karkashin jagorancin Dabid Moyes da kuma Louis Van Gaal, tun bayan ritayar, Sir Aled Ferguson a shekarar 2013.

A cewar Mourinho yayin da sauran kungiyoyin da ke fafata wasanninsu a gasar Firimiya ta Ingila, ke sayo sabbin ‘yan wasa tare da kyankyashe kwararrun matasan ‘yan wasan da suka horar, United ta fada cikin dagaji a karsahin jagorancin Moyes da Van Gaal, wanda hakan yasa united din ta kasa tafiya kafada kafada da sauran takwarorinta a Ingilan da ma sauran a nahiyar Turai.

Idan za’a iya tunawa, Daviid Moyes wanda ya maye gurbin Sir Aled Fergusson, an kore shi ne, bayan shafe watanni 10 kacal yana horar da United, biyo bayan gasa tabuka abin azo gani a wasannin kofunan ingila da kuma gaza wuce matakin kwata Final a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai.

Shi kuwa Van Gaal da ya karba, ya gaza jagorantar kungiyar ce wajen lashe kofin gasar Premier ta Ingila har karo biyu, zalika kuma ya gaza kai kungiyar halartar gasar cin kofin zakarun nahiyar turai da aka kammala.

Exit mobile version