Connect with us

SIYASA

‘Mr La’ Na Da Zimmar Sama Wa Matasa Ayyukan Yi – Muhammad Dan Auta

Published

on

Lawal Adamu Usman, (Mr. La), mutum ne wanda ya jima yana fadi-tashin ganin ya taimaka wa al’umma musamman matasan kasarnan. Na jima da sanin wannan mutumin da ake yi wa lakabi da, Mr La,’ a duk wani fanni da ya shafi taimakon al’umma. Wannan shi ne bayanin da ya fara fitowa daga bakin Muhammad Dan Auta, wanda shi ne daraktan hulda da manema labarai na rundunar yakin neman zaben, Lawal Usman Adamu, a matsayin dan majalisar Dattawa mai wakiltan mazabar Kaduna ta tsakiya.

Muhammad Dan Auta ya ci gaba da cewa, Allah Ya jefa tausayin al’umma musamman talakawa a zuciyar Mr. La, tun da jimawa, tun ma a lokacin da bai taba mafarkin zai shiga harkar siyasa ba. Kasantuwarsa dan kasuwa mai zaman kansa, wannan ya ba shi daman yin hulda da jama’a ta fuskoki daban-daban, wanda kuma duk wanda ya yi hulda da shi za ka ji yana matukar yaba masa.

Allah Ya yi masa ludufi na abin duniya, ya kuma duba ya ga cewa, wannan abin da ya samu ba karfin sa ne ba, ba kuma wata dubara ce ta shi ba, wanda hakan kuma ya sanya Allah Ya jefa masa tausayi da sanin ya kamata na ya taimaki duk wanda ba shi da shi, a taimaki wanda ba shi da karfi, a janyo wanda ba shi da shi a dora shi a kan hanyar da zai taimaki kansa ya tsaya da dugadugansa har ma ya taimaka wa sauran al’umma. Na ga wadannan abubuwan, al’umma kuma ta shaidi hakan tun kafin ma fara tafiyarsa a cikin harkokin siyasa.

Wadannan abubuwan ne muka gani a tare da shi, wadanda muka tabbatar da cewa, in har Allah Ya sanya jama’a suka yarda suka zabe shi, muna da tabbacin jama’an za su amfana da wakilcin da zai yi masu fiye da amfanan da suke yi da shi tun da jimawa a harkokin sa na kasuwanci da sauran sassan da yake yin hulda da al’umma.

Lawal Usman Adamu, mutum ne mai zimmar taimaka wa matasa da kuma sama wa matasan ayyukan yi, wanda muna da tabbacin in har ya kai ga zama a kujerar Sanatanmu, zai sama wa matasa ayyukan yi a duk mukaman da ake kebewa ‘yan majalisun dattawa a mataki na tarayya da ma na Jiha, domin ba zai siyar da su ba kamar yanda wasu suke yi. A yanzun haka, yana da gidauniya ta shi ta kashin kansa wacce yake tafiyarwa da dukiyar da Allah Ya ba shi tun da jimawa, wacce ake kira da, ‘Mr. La Care,’ wacce a cikinta ake koya wa matasa maza da mata sana’o’in hannu ta yadda za su zamo masu dogaro da kansu. Kowace karamar hukuma mutane 6,000 ne aka kebe domin a koyar da su sana’o’in. Wanda kuma bayan an koyar da su, duk wadanda suka mayar da hankali wajen koyon za a tallafa masu da jarin da za su kafu da kansu wajen yin sana’ar da suka koya.

Na kuma ji dadin tsintan kaina a cikin tafiyar mutum irin wannan, wanda tabbas irin sa ne muke nema wadanda muna da tabbacin al’umman ne a cikin zukatan su. Duk abubuwan da nake fada a baya, musamman a Jam’iyyarmu ta PDP, na cewa a zabi mutumin da ya dace, ya cancanta, ya san mutuncin jama’a yake kuma neman ya ga ya daga wasu ta yadda su ma za su tsayu da dugadugansu, sai Allah Ya sanya na gansu a tare da wannan bawan Allah mai suna Lawal Adamu Usman.

Wannan shi ne dalilin da ya sanya na ji dadin tsintar kaina a cikin wannan tafiyar na shi na hankoron kaiwan shi wancan matsayin da na tabbbatar da cewa mutane ne za su amfana

 
Advertisement

labarai