Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NAZARI

MUƘALA: Hattara Dai Inyamurai (5)

by Tayo Adelaja
October 27, 2017
in NAZARI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A cikin wannan hali aka je zaɓe a cikin watan Disamba 1964 tsakanin waɗannan jam’iyyu guda biyu inda kowa ya shiga nuna ƙwarewarsa a siyance. A nan arewa tun kafin a fara zaɓe masu takarar UPGA guda 67 suka janye don sun tabbatar da cewa ba za su kai labari ba. Wannan abu ya ruɗar da manyan jam’iyyar UPGA inda suka ce a ɗaga zaɓe wanda sam ba zai yiwu ba don jam’iyyar siyasa ba ta da hurumin ta ɗaga zaɓe sai dai ita hukumar zaɓe ta ɗaga in tana da wani ƙwaƙƙwaran dalili.

Daganan ko sai ‘yan jam’iyyar UPGA suka yi wani hauka inda suka umurci ‘ya’yansu da kada su je wajen zaɓen wanda ya sanya NNA ya kayaye zaɓe a fayu. Sai daga baya manyan UPGA suka gane cewa hakika sun yi hauka kuma ba su yi amfani da hankali ba, amma abin sai ya koma kuwwa bayan hari. A arewa dai an fita zaɓe inda aka yi shi tsaf. Can kuma a ƙasar Yarabawa ‘yan jam’iyyar NNA sun je su kuma ‘yan UPGA suka ƙi zuwa wanda ya sanya can ma NNA ya share mafi yawan kujerun. Kwatankwacin wannan abu ne ya faru a jihar tsakiyar yamma. Amma a ƙasar Inyamurai Firimiya Okpara ya yi amfani da ƙarfin mulki ya hana zaɓen. Can daga baya da aka natsa aka ce babu inda za sake zaɓe in ba wuraren da ba a yi zaɓe ba a baya wanda ya sanya ƙasar Inyamurai ne kawai  aka bayar da iznin a gudanar da zaɓen inda aka yi shi a ranar 18 ga watan Maris 1965 kuma UPGA ta kayaye dukkan kujerun su 51 ɗin da kuma kujeru 3 a Ikko. Shike nan suka koma ‘yan adawa.

samndaads

Bayan wannan ne Yarabawa suka ƙara tayar da ƙayar baya inda suka yi ta kashe ‘yan uwan su Akintola watau Yarabawan nan masu babbar tsaga irin ta Gobirawa wanda ya sanya mafi yawansu suka tsero suka dawo arewa inda suka zauna cikin salama har zuwa yau don wasu ma sun koma ‘yan ƙasa a inda suke zaune.  Wasu daga cikinsu yanzu da wuya mutun ya iya gane cewa su Yarabawa ne don wasu ma sun mance yarensu sun koma Hausawa. Ganin haka ya sanya Zik ya cewa ɓalewa da ya kafa gwamnati.

Da mutanen kudu suka ga sun buga abin ya fi ƙarfinsu kuma suka gane cewa duk dabararsu babu yadda za su iya ƙwace mulki daga hannun arewa ta hanyar siyasa sai suka sake sabon salo inda suka yi shawarar su ƙwace mulkin da ƙarfin soji su kuma yi wa shugabannin arewa kisan gilla. Wannan ya sanya suka samu sojoji ‘yan ta-kife waɗanda suka san da ma ba su ƙaunar waɗannan shugabanni suk cusa musu wannan ra’ayi da sunan juyin-juya hali. Waɗannan matasa ko kuma ma in samari majiya ƙarfi ne kuma dukkansu suna da muƙamin Manjo a cikin rundunar sojan Najeriya. Aka ɗora waɗannan matasa kayan da ba su san ko mene ne ba kuma ba su san inda za a kai kayan ba. Sai da suka kai inda ake son su kai sa’annan aka kame dukkansu aka zuba a jarun daga baya kuma suka yi mutuwar wulakanci.

Kamar yadda Wale Ademoyega wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda aka sanya wannan dakon fitina ya ce a cikin littafinsa Firaminista da Firimiyoyi yankunan uku ne kaɗai suka yi niyyar kamawa. Bayan su kuma sai manyan sojojin da ke goya wa su ‘yan siyasar baya. Daga cikin waɗanda ya ce za kama akwai Janar J.T.U. Aguiyi Ironsi da Birgediya Ademologun da Birgediya Maimalari da Kanar Kur Mohammed  da Kanar Shodeinde  da Lt. col. Pam  da kuma Lt. col. Unegbe waɗanda dukkansu manyan sojojin Najeriya ne a lokacin.

Amma bayan shi sai Aleɗander Madiebo wanda shi ma soja ne wanda ya samu tsallake rijiya da ƙundun baya a lokacin ramuwar gayya kan Inyamurai ya faɗi gaskiya a cikin littafinsa inda ya ke cewa ‘a lokacin wannan ta’asa sai shi shugaban shirin ya zaɓi Emmanuel Ifeajuna da Anuforo da Donatus Okafor da kuma Wale Ademoyega wanda da ma can suna da wata jiƙaƙƙa da manyan sojojin da ke can Ikko.

Kafin su kai ga wannan aika-aika sai da Manjo Chukwuemeka Kaduna Nzeogwu ya yi ta yin wani atisayen soja cikin dare tare da waɗanda za su yi wannan ta’asa amma babu wani sojan da ya san manufarsu ana tsammanin rawar daji ce kawai ta soja. An fara wannan a Ikko amma Birgediya Maimalari na gani ya hana tun kafin abin ya yi nisa. Amma a Kaduna aka bari suka yi ta yi kwanaki masu yawa.

A ranar da za su yi wannan aika-aika waɗanda za su yi ta a Ikko sun taru inda Manjo Emmanuel Ifeajuna ya yi musu jawabi ya kuma nuna musu muhimmanci wannan abu da za su yi. Bayan wannan sai aka raba wa kowa aikin da zai yi. Shi Emmanuel Ifeajuna shi da jama’arsa ne za su kamo Firaminista Sir Abubakar Tafawa ɓalewa da kuma Ministan Kuɗi Mr Festus Okotie-eboh kamar yadda suka ce, amma abin mamaki bayan sun kamo ba tare da samun turjiya ba ko kaɗan sai suka yi wa waɗannan bayin Allah kisan gilla.

Shi kuma Manjo Anuforo shi da jama’arsa za su kamo Kanar Kur Mohammed da kuma Lt. Unegbe. Shi kuma Manjo Okafor shi da jama’arsa zasu kamo Janar Ironsi da Birgediya Maimalari.

Manjo Chukwuka shi da jama’arsa za su kamo Lt. col. Pam, Manjo Ademoyega kuma shi da jama’arsa su tsare wurare masu muhimmanci ga sadarwa da suka haɗa da hedikwatar ‘yan sanda da hedikwatar sadarwa ta P&T da kuma gidan Rediyon Tarayya. Bayan wannan kuma shi Manjo Ademoyega ne zai yi jawabi da safe in abin ya gama cin nasara.

Bayan raba aiki sai kowannensu ya kama hanya zuwa wurin yin wannan aika-aika. Sa’annan kuma suka aika da signal zuwa Abeokuta inda suka umurci wakilinsu na can mai suna Nwobosi da ya ci gaba da aiki. Haka kuma aka aika a Enugu shi ma a can suna da wakili mai suna Oguchi ya fara. Da ƙarfe 2 na dare suka kama hanyoyin zuwa aika-aikar, da ma can sun riga sun shirya yin komai a lokaci guda.

Da farko yana cikin wannan bilinbituwa ne ya gamu da Anuforo da jamar’asa suna dawowa waɗanda suka ba shi albishir ɗin cewa sun gama nasu aiki kuma ya ci nasara. Suka ce masa sun kam Kanar Kuru Mohammed amma shi Lt. col. Unegbe ya ƙi yarda a kama shi saboda haka sun kashe shi.

Daganan kuma sai ga Manjo Chukwuka ya zo ya ce shi ma ya ci nasarar gama nasa ya kuma kamo Lt. Col. Pam. Sai kuma ga Manjo Emmanuel Ifeajuna su ma sun ci nasara sun kamo Firaminista da Ministan kuɗi Chief Festus Okotie-eboh. Lokacin da suke dawowa ne kuma suka ga Birgediya Maimalari yana neman tserewa saboda shi ma suka kashe shi ko da ya ke su Okafor ya kamata a ce sun kama shi. Ina son Mai karatu ya gane cewar duk waɗannan da aka kashe babu Inyamuri ko guda a cikinsu sauran ƙabilun Najeriya ne.

Daganan sai kuma ya tafi wajen Donatus Okafor da jama’arsa inda suka gamu yana fitowa daga cikin barikin soja. Sai Ademoyega ya tambaye shi abin da ya faru sai shi Okafor ya ce wai bai ci nasarar kame Janar Ironsi ba wanda shi Ironsi Inyamuri ne, kuma wai har RSM ya so kashe shi. Nan dai ya shiga kawo wa Ademoyega bayanai marasa kan gado wanda duk wanda ya karanta yadda abin ya wakana ya san da walaki goro cikin miya. Wannan ya isa ya nunawa Mai karatu cewa wannan wani shiri ne aka yi na ba shi hanyar tserewa don shi Inyamuri ne aka kame waɗanda ake so a kama. Shi kam Donatus Okafor bai ci nasarar yin komai ba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Za Mu Ci Gaba Da Fafutukar Neman Haƙƙoƙin Mu –’Yan Fanshon ABU

Next Post

NDE Ta Ƙaddamar Da Taron Haɓaka Aikin Yi Ga Matasa 18,000 A Kebbi

RelatedPosts

Dan Uwan Minista

Ayyukan Ta’addanci A Arewacin Nijeriya

by Sulaiman Ibrahim
13 hours ago
0

Ga duk mai tabaraun hangen nesa, zai fahimci cewa lallai...

Sarkar Da Za Ta Sarke Kaduna Bayan Amsar Bashin Dala Miliyan 350 Daga Bankin Duniya

Sarkar Da Za Ta Sarke Kaduna Bayan Amsar Bashin Dala Miliyan 350 Daga Bankin Duniya

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Daga Dr. Nasiru Aminu “Babu al’ummar da za ta kasance...

National Economy

Shekara Daya Da Fara Fitowa: Gudumawar Jaridar NATIONAL ECONOMY Ga Tattalun Azikin Nijeriya

by Muhammad
7 days ago
0

Daga Khalid Idris Doya, A jiya Asabar ne jaridar NATIONAL...

Next Post

NDE Ta Ƙaddamar Da Taron Haɓaka Aikin Yi Ga Matasa 18,000 A Kebbi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version