Daga Idris Aliyu Daudawa
Lokacin da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ke shirin bada bayanin abubuwan da ya san sune, musabbabin dalilan da suka shay a sha kaye a zaɓen 2015, duk da haka kuma da akwai ‘yan cikin gida waɗanda suma sun san dalilian da suka sa a har aka sha kaye.
Gwamna Nyeson Wike na jihar Riɓers ya ce wasu daga cikin ‘yan majalisar zartarwarsa, da kuma manayan da ke faɗa aji a jam’iyyar PDP, da shi tsohon shugaban jma’iyyar Adamu Mu’azu, sun yaudari tsohon shugaban ƙasar, saboda sun faɗa mai ƙaryar shi ne zai samu nasara.
Ita dai wannan tattaunawar da aka fitar Wike ya ce ‘’ Bari in faɗa maku gaskiya yawancin mutane sun yi ma Jonathan yaudara. Ya ce idan ma mutum yay i la’akari da yadda abubuwa suka tafi, mutane da yawa munafunci ne suka yi amfani da shi.’’
Wike ya ƙara jaddada cear akwai lokacin da ‘yansiyasa ya kamata ace suna su fita fagen daga, amma sai suka yi zaman su a Abuja, daga nan ne kuma zasu riƙa fitar sakamakon ƙanzon kurege, har ka ji sun a cewa’’Rankai daɗe wallahi kamar yadda nake maganada kai yanzu jihohi masu yawa PDP ce gaba’’.
Ya ƙara da cewar al’amuran duk ƙarya ne ya kuma nuna rashin jin daɗinsa da shugabannin Arewa waɗanda ya ce basu yi ma PDP adalci ba, musamman ma a Arewa. Suka haɗe ma Jonathan kai, gaskiya ba wta maganar adalci basu ƙyauta ma shi ba.
Wannan ba ƙaramin mugun haɗin kai aka yi ma Jonathan ba, saboda ya ƙara da cewar ai akwai jihohin ma da aka jefi shugaban ƙasa, kuma gwamnonin su ka sa ido suna kallo, kuma idan shi ne Jonathan ba zai yarda ba.
Wike dai shi ne ƙaramin ministan ilmi lokacin mulkin Jonathan, bugu da ƙari kuma an san cewar shi ne ɗan gaban goshi uwargidan tsohon shugaban ƙasar Dame Patience Jonathan.
Da yake shi ne shugaban sasanta ‘yan jam’iyya waɗanda aka ɓatamawa ya ce a taronsu na jam’iyyar sun zargi, manyan ‘yan babbar jam’iyyar adawa, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ana zargin suma suna da hannu .