Connect with us

LABARAI

Mu A Kaduna Zaben Daliget Zamu Yi – Jam’iyyar APC

Published

on

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kaduna, ta bayyana cewa a zaben fidda gwani da jamiyyar zata gudanar ba zata gudanar da tsarin zabe na kato Bayan kato ba, bisa dalilan tsaro da na kudi.

A wani taron masu ruwa da tsaki a jam’iyyar wanda mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Barnabas Bala Banted, da Shugaban jamiyyar APC na jihar suka jagoranci gudanar shi, jamiyyar ta ce sun jaraba tsarin zaben kato Bayan kato A zabukan kananan hukumomin jihar a watannin baya ba’a samu nasara wanda hakan ya haifar da rikici.

Jam’iyyarta kara da cewa idan ta gudanar da zaben fitar da gwani na tsarin kato-bayan-kato babu shakka za’a samu matsaloli masu yawan Gaske bisa la’akari da cewa har yanzu jamiyyar APC bata tan-tance adadin masu dauke da katin jamiyyar ba.

Kakakin majalissar dokokin Jihar Kaduna, Honaraul Aminu Shagali, wanda yana daga cikin wadanda suka karanta sakamakon bayan taron ya bayar da tabbacin cewa gudanar da tsarin zabe na wakilai shi ne Kadai hanyar da jamiyyar zata bi domin gudanar da sahihin zaben fidda gwani.

Shagali, yace zaben kato Bayan kato yana bukatar kashe makudan kudade inda yace akalla za’a kashe kudi sama da naira miliyan dubu wanda a cewarsa, jamiyyar a halin yanzu bata da irin wannan kudi.

Ya ci gaba da cewa “Kamar yadda uwar jam’iyyar APC ta tsara na gudanar da zabukan fidda gwani na jam’iyyar a matakai daban – daban a jihar.

Taron wanda shi ne karo na takwas , ya samu halarcin mataimakin Gwamnan jihar Kaduna, Barnabas Bala Banted da Shugaban Majalisar Dokokin jihar Kaduna, Aminu Shagali da Sanata Shehu Sani da ‘yan majalisun dokokin jihar da ‘yan majalisun Tarayya da kuma shugabannin kananan hukumomin jihar da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC na Jihar Kaduna.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: