Mu A Wurin Allah Muke Neman Wannan Kujera Ta Gwamna -Sarki Labaran

Injiniya Sarki Labaran gogaggen dan Siyasa, Tsohon Kwamishina a Lokacin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, kwararren injiniya, wanda gudunmawarsa da tallafinsa ya kai ga marayu da marasa galihu mausamman aloakcin a zumin Ramadan. A tattaunawarsa da Wakilinmu a Kano Abdullahi Muhammad Sheka, Injiniya Sarki Labaran ya bayyana halin da takararsa ta Kujerar Gwamnan Jihar Kano Kakashin Tutar Jam’iyyar PDP ke ciki, sannan kuma ya bayyana gazawar Gwamntin APC musamman a Jhar Kano, wanda yace al’umma ba zasu manta da Gwannatin Shekarau ba. Ga dai yadda tatattaunawar ta kasance:

Za muso jin Wanda Muke Tare dashi?

Alhamdulillahi ni dai Sunana Alhaji Sarki Labaran tsohon Kwamishina a Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, mai tsawatarwa a Kungiyar masu bukatar Jam’iyyar PDP  a Jihar Kano ta tsayar dasu takarar Gwamnan Kano a zaben shekara ta 2019 idan Allah ya kai mu.

Yanzu haka da aka fara kada kugen siyasar shekara ta 2019 labari ya bayyana yadda kungiyoyi da kuma dandazon matasa keta rajin kiranka domin fitowa takarar kujerar Gwamnan Jihar Kano, shin me ake ciki kan wannan bukata ta al’ummar Kano?

Haka ne, kamar yadda ka sani shi halin mutum akace jarinsa wannan kiraye-kiraye  suna zuwa kunnemu, kuma muna tayi wa jama’a bayani cewar shi komai da lokacinsa, amma dai abinda kullum nake fadawa masoya shi ne a kara hakuri muga yadda harkokin siyasar zasu kasance, kuma ina tabbatarwa da jama’ar Kano cewa insha Allahu ba zamu watsa masu kasa a ido ba. Idan lokaci ya yi zan magantu da yardar Allah.

Amma fa akwai matsala domin an fara jin muryoyin wasu matasan dake shata layin cewa matukar kaki amincewa  da wannan bukata ta Jama’a, ko shakka babu sun tanadi duk abinda ake bukata wajen gurfanar da kai gaban kuliya, domin acewarsu ba zasu bari a sake shan su basulla ba, me zaka ce kan haka?

To! Abin har ya yi zafi haka, bari in tabbatarwa da wadanan masoya cewar su sha kuruminsa  Sarki Labaran ba don kansa yake siyasa ba, tunda al’umma sun nuna haka ina tabbatar masu da cewa zan amsa wannan kira, kuma muna neman wannan Kujera a wurin Allah ba wani ba, da yardar Allah dan nasu ba zai basu kunya ba, su kwantar da hankalinsu ba sai ta kai ga zuwa gaban kuliya ba.

Amma dai ina kara jadaddawa jama’a cewa su sani shi komai da kake gani tsari ne daga Allah sai abinda yaso ke gudana, don haka ba muda wani wayo ko dabara akan haka, saboda haka mun mika komai awurin Allah shi muke nema a wurinsa, kuma muna da yakinin zai dubi kyakkyawar niyyar mu ya ci ka mana wannan buri na alhairi domin taimakwa jama’a gwargwadon iko.

Idan Allah ya baka wannan dama a matsayinka na wanda ya kasance cikin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, wadda al’umma suka shaida gudanar da harkokin Gwamnati tare da kowa da kowa ta ina zaka fara, kasancewa akwai abubuwa da dama wanda suka yiwa jama’a batan dabo a aikace a Jihar Kano?

Alhamdulillahi ina kara jajantawa al’ummar Kano irin halin da muka tsinci kanmu a ciki duk da cewar Jihar Kano jiha ce da Allah ya Tarawa tarin albarka, amma mun ka sa gane a ina gizo ke sakar daga mu ne ko shugabannin da aka zaba a matakai daban daban. Wanann tasa  dole mu fito domin nemawa jama’a makoma domin Jam’iyyar APC ta ka sa.

Duk da irin dimbun dukiyar da ake rajin wai an kwato daga hannu wadanda ake kallo a matsayin barayi, amma har yanzu bata sake zane ba, Alhamdulillahi jama’ar Kano sun ga yadda aka gudanar da gwamnati a lokacin Malam Ibrahim Shekarau, kuma irin wannan tsarin a jinin jikinmu yake. Don haka akwai abubuwa da yawa wanda idan Allah ya dawo da mulki hannun Jam’iyyar PDP kowa zai gani a kasa wai da aka ce ana buki a gidan su kare yace na gani a kasa.

Idan muka kalli Gwamnatin Ganduje a shekara uku data yi akan karagar mulkin Jihar Kano, me za kace an gani a kasa ta fuskar ci gaban al’umma?

Wannan tambaya kamata ya yi ace jama’ar Kano aka yiwa ita domin wai da bahaushe ke cewa jiki magayi, daman shi shugaban Kasar sai da ya fadi cewar kowa sai yaji a jikinsa, kuma gashi ana ta faman gasawa talakawa aya a tafin hannu. Mu a Jihar Kano babbatar matsalar mu itace

makauniyar soyayya, alhamdulillahi shi gwamnnan dake kan karagar mulki tun zuwansa kan wannan kujera ya shelanta cewa zai dora akan aikin kakansa, kuma mun gani ya kara sa wasu manyan ayyuka, duk da daman gwamnatin Mu a wancan lokacin ta gama komai da komai fanti da zuba kayan aiki suka rage.

Amma mu tsari irin namu shi ne inganta rayuwar al’umma na cikin abubuwan da zamu fi mayar da hankali, domin mutun shi ne ruhin duk wani ci gaba da ake bukata, samar da kyakkyawan nutsuwa ga al’umma ne ke haifar da kyakkyawan tunani, saboda idan Allah ya bamu wannan dama zamu karkade ajiyar mu domin dorawa akan abubuwan cigaban da muka gudanar a glokacin da Allah ya ara mana irin wannan dama.

Ranka ya dade ana ganin kamar masu zawarcin wannan kujera a Jam’iyyar taku ta PDP a Jihar Kano sunyi yawa, baka ganin hakan ka iya haifar maku da matsala alokacin zaben fidda gwani?

Ina tabbatar maka da cewa mu masu neman Sahallewar Jam’iyyar PDP takarar Kujerar Gwamna a Kano duk kanmu a hade yake, kuma yanzu haka mun samar da wani dandamali na ‘yan takara wadda ni ne ma mai tsawatarwa a wannan kungiya. Saboda haka ba mu da wata matsala, ina tabbatarwa da jama’ar Kano musamman ‘yan Jam’iyyar mu ta PDP mai albarka cewar kowa ya sha kuruminsa wajen fitar da dan takara ba wata matsala.

Ana ganin kamar abubuwan da Jam’iyyar PDP ta gudanar a  lokacin mulkin ta na tsawon shekara goma sha shida, akwai abubuwan da ake alakanta su da Jam’iyyar taku wadda a ganin Jam’iyya Mai Mulki ba wanda zai amince da kara zabar PDP, shin ko ya kake kallon wannan hange ko na ce zargi?

‘Yan Jarida Ke nan ai daman Bahaushe na cewa kar Allah ya kawo ranar yabo, cewa akayi gwamnatin PDP gwamnatin barayi ce, ba tsaro, babban abinda nake son tambayar masu irin wancan adawa shi ne, idan dai Gwamantin PDP ce ta kawo matsalar rashin tsaro karkashin tsohon shugaban kasa Jornathan, to dole a yarda cewa Gwamnatin APC Karkashin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ce ta kawo yunwa da sauran abubuwan da ke faruwa a wannan lokaci.

Kamata ya yi Jam’iyyar APC ta mayar da hankali kan gazawar tan a cika alkawurran data yiwa talakawa, musamman na kawo karshen matsalar da suke ce Gwamnatin PDP c eta Kawo ta, sannan su mayar da hankali wajen duba halin da talakwa suke ciki a halin yanzu wanda wata Hukuma ta Duniya ta tabbatar da cewa yanzu talakawan da ke kwana da yunwa a Nijeriya sun zarta na   kasar indiya, rahoton ya nuna cewa duk minta guda talakawa shida ke kara tsunduma cikin halin tsaka mai wuya a Nijeriya.

Mene ne Sakon ka ga Al’umamr Jihar Kano wadanda kake neman sahallewarsu

domin zabar ka a matsayin Gwamnan Jihar Kano?

Alhamdulillahi babban sakona ga Jama’ar Jihar Kano shi ne su fahimci cewa yanzu fa kowa naji a jikinsa, kuma akwai hadisi wanda ke nuna cewa mumini baya bari maciji ya cijeshi a rami guda sau biyu. Saboda haka ya kamata jama’ar Kano suyi karatun baya, suyi la’akari da abinda

wadanda ke cikin wannan Jam’iyya suka yi alokacin da suke kan karagar mulki, su tsaya tsai su tantance masu irin wannan bukata, kuma su dorasu akan sikeli domin tabbatar da zabar wadanda zasu kyautata rayuwarsu.

Saboda haka ina kara jajantawa Jama’a halin da aka tsinci kai a ciki karkashin Mulkin APC, musamman ma yaudarar da ake yiwa jama’a na batun rajin yaki da cin hanci da rashawa, wanda sai ‘yan Jam’iyyar adawa ake yiwa tonon silili, dubi irin abinda ake yiwa tsohon Gwamnan Kano mai gidanmu Malam Ibrahim Shekarau, kuma abin dariya duk abinda ake

tuhumarsa shi ne miliyon 25, wanda ya yi gwamna tsawon shekara takwas, kuma kudin da aka ce an raba a gidansa Naira Kusan Miliyon 950, amma Naira Miliyon 25 ake zarginsa Ai kasan wannan so ake kawai sai an tozarta masu cikakken farin jini a tsakanin al’umma.

Don haka nake kara jan hankalin jama’ar Kano da cewar mun fito wannan takara ba ko a mutu ka ayi rai bane, nema muke a wurin Allah, muna kuma kyautatawa Allah zaton alhairi a gare mu.

 

Exit mobile version