Mu Ci Gaba Da Gudanar Da Addu’o’i Domin Shawo Kan Matsalolin Tsaro – Imam Ibirahim

Addu'o'i

Daga Bala Kukkuru,

Babban limamin masallacin juma’a ta izalatul-bidi’a wa’ikamatus sunna ta kasa reshen jihar Legas da ke tsibirin rukunin gidajen unguwar wantauzan a cikin garin ikko, lmam Ibirahim suleman, kuma shugaban kungiyar izalatul-bidi’a, ya shawarci al’ummar musulmi da kiristoci da sauran jama’ar Nijeriya da su cigaba da gudanar da addu’o’i na musamman domin taya Gwamnati shawo kan matsalolin tsaro da zaman lafiya a duk fadin kasar nan.

Babban limamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gudanar da tafsirin kur’ani na azumin wannan watan na Ramadan mai albarka na bana, wanda ya saba yi a kowace shekara a daidai wannan lokaci na watan Ramadan, domin fadakar da al’ummar musulmi abubuwan da ake son musulmi ya aikata a cikin watan mai tsarki da sauran aiyukan alheri.

Ya cigaba da cewa, ya zama dole al’ummar musulmi su bada ta su gudummawar ta addu’o’i na musamman a cikin wannan watan mai tsarki domin tallafawa Gwamnati ta samu sauki wajen shawo kan tsaro a kasar.

Haka zalika, ya shawarci ‘yan kasuwa musamman wadanda suke kara farashin kayan abincin da al’ummar musulmi ke amfani da su wajen sahur da budabaki da su ji tsoron Allah azukatansu wajen gudanar da al’amuransu na kasuwanci da kuma yau da kullum.

Ya kara da cewa, “bai kamata ace dan kasuwa kuma musulmi mai son rahamar ubangiji a ranar gobe kiyama ya kasance yana kara farashin kayan abinci ba, wanda akasari al’ummar musulmi ne ke amfani da shi a wajen sahur ko kuma budabaki. Da fatan ‘yan kasuwa masu irin wannan hali za su cigaba da jin tsoron Allah su daina aikata irin wadannan miyagun halaye.”

Ya ce, haka kuma, manyan masu kudin kasar nan da sauran al’umma masu hannu da shuni suma yakamata taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa al’ummar musulmi a cikin wannan wata mai tsarki. Sannan kuma yana mai farin cikin taya ‘yan uwa musulmi murnar zagayowar wannan watan na Ramadan da al’ummar musulmi suke gudanar da ibadunsu tare da neman falalar samun duniya dama lahira baki daya.

A karshe ya ce, yana yiwa dukkan al’ummar musulmi fatan alheri wajen kammala wannan ibadar lafiya.

 

Exit mobile version