Bala Kukkuru" />

Mu Cigaba Da Addu’o’in Zaman Lafiya A Wannan Shekara – Sarkin Yarabawan Funtuwa

Sarkin Yarabawan Funtuwa

Mai Martaba Sarkin Yarabawan yankin Karamar Hukumar Funtuwa a Jihar Katsina kuma jagoran al’ummarsa ta Yarbawan a garin Funtua, Injiniya Alhaji Murtala A. Sani, ya shawarci al’ummar Karamar Hukumar Funtua da Jihar Katsina da sauran jihohin Arewacin Nijeriya da Nijeriya baki daya da su cigaba da gudanar da adduoi na musamman domin neman karin zaman lafiya a kasar nan bakidaya.

Sarkin Yarabawan ya yi wannan bayani ne a ofishinsa da ke cikin garin Funtua jim kadan bayan kammala ganawarsu da wadansu al’ummar Yarabawa da na Hausawan garin yayin da suka kai masa ziyara, inda ya yi ga jama’a kan muhimmancin zaman lafiya, inda ya ce, yakamata al’ummar kasar nan su cigaba da yin addu’a don neman karin zaman lafiya domin zaman lafiya shi ke kawo yalwatuwar arziki da kuma sanya nutsuwa a zukatan al’umma.

“Shawo kan sha’anin tsaro a Nijeriya ba wai gwamnati kadai take da hurumin daukar matakan shawo kansa ba, su ma al’umma suna da muhimmiyar rawar da ya kamata su taka.

Ya cigaba da cewa a kan haka yake ganin ya kamata ya shawarci al’ummar kasar nan da su dunkule su cure su zama tsintsiya madaurinki daya a wajen gudanar da adduoi tare da suffatuwa da kyawawawan dabiu domin ya zama darasi ga yara kanana na baya masu tasowa baki daya da.

Da yake tsokaci a bisa yanayin kyautata mu’amala tare da halin zaman takewa a tsakanin al’ummar Hausawa da na Yarabawa mazauna yankin garin funtuwa kuwa, cewa ya yi babu shakka tsakanin al’ummomin guda biyu suna fahimtar juna tare da cikakken hadin kai tare da jituwa a tsakaninsu.

Ya ce domin kuwa tun daga lokacin da yake yaro zuwa yanzu bai taba ganin wani abu na bacin rai ya hada wani Bahaushe ko Bayerabe game da tashin hankali ko abin da ya yi kama da hakan ba, haka zalika, suna zaune lafiya babu abin da za su yi wa Allah sai godiya, daga nan kuma ya shawarci al’ummomi dasu cigaba da hada kawunan junansu kamar hakan yadda suka saba domin su kara samun zaman lafiya a tsakaninsu. Daga karshe ya ce yana yi wa duk kan al’umma fatan alheri tare da murnar shigowar sabuwar shekara kuma da fatan Allah Ya cigaba da zaunar da Nijeriya lafiya.

 

Exit mobile version