Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu, ya jagoranci yiwa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje addu’a ta musamman a babban Masallacin Juma’ar Kano bayan da ya lashe zaben gwamnan jihar kano a karo na biyu.
Daga cikin wadanda suka halarci taron addu’ar sun hada da Dagatai, manyan Limamai, Malamai, manyan ma’aikatan gwamnatin jihar, masu bada shawara ta musamman da sauran al’umma.
A cewar sarkin, addu’ar ta neman kariya ce da neman jagorancin Allah a mulkin da gwamnan zai yi karo na biyu da ma kasa baki daya.
Mai martaba ya bayyana cewa; yafiya wajibi ce a dukkan wani abu da ya shafi shugabannci da mu’amala da mutane.
‘Ba laifi bane wani ya rike ra’ayin shi akan abun da yake faruwa a cikin al’umma, amma abun da ya zama dole bayan zabe shine mutane su hada kansu wajen tabbatar da mulkin wanda yayi nasara.
‘Saboda haka, ya zama wajibi gwamnatin Ganduje ta samu goyan baya da hadin kan al’umma dan cigaban jihar mu.
‘Dole sai mun hada kan mu da cigaban jihar Kano. Sai mun yi aiki tukuru da kuma dagewa da addu’a dan cigaban jihar mu da kasa baki daya.’ inji shi
Ya yi kira ga gwamnan da ya dinga yin bincike a dukkan wani labari da yaji dan wani lokacin mutane suna kirkirar labarai sannan su fara yada jita jita dan sun haifar da rikici.
Mai Martaba ya kara da cewa; Wani lokacin mutane sukan yi abu ba tare da sanin ka ba amma sai wasu su fara yada jita jitan cewa kai ka shirya wannan abun, kuma alhalin baka da masaniya akan abun, sabodahaka, mu ci gaba da yiwa Kano adduár zaman lafiya, ya kuma kara da cewa shugaba dole ya zama na kowa.