Assalamu Alaikum warahmatullah. Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa da komai.
Zan yi amfani da wannan dama, musamman bisa la’akari da irin yanayi na annoba da muka tsinci kanmu ciki ahalin yanzu .
Wannan annoba ta cutar Korona, annoba ce da ta zagaye duniya gabaki dayanta.
Tabbas idan muka yi la’akari da illar da ta yi ga kasashen da suka ci gaba toh ya kamata mu kiyaye da bin shawarwari da bin dokokin masana da gwamnati domin mu kauce wa fadawa irin halin da wadancan kasashe suka fada. .
Mun yi matukar yabawa da kokarin gwamnati na kokarin kare rayuwaka da lafiyar al’ummah.
Bin wannan doka ita ce mafita da yardar Allah, toh amman idan muka duba za mu ga mafi yawancin mutanen dake kasar nan musamman yankin Arewacin Nijeriya suna rayuwa ne a kan sai sun fita sannan su samo abin da za su ci da iyalansu.
Mu yiwa kawunanmu tambaya akan to su wayyannan mutane me za su ci ko yaya za su yi idan har basu fita neman ba?
Tabbas gwamnati da masu hannu da shuni da kungiyoyin sa-kai suna kokari, amma mu sani wannan ba hakkin gwamnati bane ko masu kudi akwai hakki ne daya rataya akan kowa muddin kana da iko komi kankantarshi, toh ina ganin ya wajabta mu fito mu taimaki masu raunin cikinmu.
Idan Kana da niyyar taimako, toh kana yin sa ne daidai ikon ka.
Misali da ni kaina a nan, malamar makaranta ce toh amman sai na ga idan har zan iya ajiye ragowar kudi sai nike ganin tabbas na yi rashin imani kuma na so kaina da yawa idan har akwai wani a kusa da ni da ke jin yunwa a irin yanayin da muka tsinci kanmu, in da na yi amfani da albashina na watan maris wajen siyan kayan tallafi ga ‘yan’uwa da makwabta na kusa da nesa.
Sai na fahimci a cikin masu tururuwar zuwa neman sadakar akwai wadanda suka fi ni da yawa. Tabbas na dada fahimtar cewa akwai mabukata dayawa, Sannan kuma mai hali baya hakuri yabarwa Mara hali .
Wannan dalili yasa mukayi shawarar kafa kwamiti me suna “taimakon mabukata” watau a turance muka kirashi (help the needy) a karkashin kungiyar sulhu da kyautata zamantakewar iyali (help for bictims of matrimonial Abuse foundation)
Mun kudurci anniya da yardar Allah daukar nauyin ciyar da gidajen da suke matukar bukata ta la’akari da yadda za mu shiga watan Ramadan kuma kudurinmu ba zai tsaya a iyakacin Ramadan ba insha Allahu.
Yawan gidajen da za mu dauke wa nauyin ciyarwar zai dangantane da karfin asusunmu tun daga ranar da aka fara azumin watan Ramadan har karshensa da iznin Allah.
Daga karshe ina kira ga mutane da mu sani cewa ba wai sai muna da kudi za mu iya taimaka wa junnanmu ba, idan kana da abincin gobe to mu duba wanda ba shi da na cin yanzu domin goben Allah ke da ita. Mu sani cewa hannun mikawa ya fi na karba.
Wadanda gwamnati ke bawa tallafi su raba da su ji tsoron Allah gurin sauke nauyin da aka dora musu su tabbatar da sakon ya kai inda ya kamata ya je.
Idan muna da abincin yanzu toh mu yi hakuri mu bar wa wanda bai da na yanzu ya karba.
Wata shawara ga maniyyata Umurah da Aikin Hajji ita ce, tun da a bana saboda lalura da wuya wadannan ibadun su yiwu, toh ga wani aikin Allah idan har domin neman yardar Allah muke yi toh mu fito da kudaden nan domin rage wa mutane kunci da radadin rashin da suke ciki.
Mu sani cewa dukkan wanda ya fidda wani mumini daga kunci toh tabbas Allah zai yaye nasa ya sa masa albarka.
Daga karshe ina kira ga al’ummah da wallahi mu koma ga Allah mu kyautata zukatanmu, mu dimanci istigfari, mu kiyaye zalunci, ko hakan ya taimaka wajen kawar da fushin Allah a kanmu.
Muna addu’a Allah ya bamu ikon sauke nauyin da muka dauka, da fatan Allah ya biya dukkanin wadanda suke da hannu wajen taimakawa al’ummah ta kowace fuska, Allah ya biya su ya ninka masu da mafiyin alkhairi a duniya da lahira, amin summa amin.
Zainab Mohammed
Shugabar Gidauniyar Taimakon Mabukata ta ‘Help the Needy’.