Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home NAZARI

Mu Koma Gona Domin Noma Tushen Arziki Ne, In Ji Baba Akuyum

by Tayo Adelaja
September 24, 2017
in NAZARI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Harkar noma wata sana’a ce wacce idan mutum ya rungume ta kakarsa ta yanke saka, domin sana’ace wacce mutum zai samu zarafin daukan nauyin kansa, iyalansa kai zai iya taimaka wa wasu da sana’ar noma matukar ya maida hankali kan nomar nan.

Jihar Bauchi ta kasance jiha wacce Allah ya azurtata da albarkatun gona, ma’ana al’umman jihar suna ribantar sana’ar Noma sosai. Allah kuma na basu yalwa sosai inda zaka tarar suna girbe riba sosai ta wannan bangaren na Noma. Jihar Bauchi jiha ce wacce al’umman jihar su ka rungumi bangaren noman masara fiye da sauran kayyakin abinci. Sai dai, al’umman yankin Bauchi ta Kudu sune suka fi Moman Masara, a yayin da sauran bangarorin jihar kamar Bauchi ta Arewa su kuma suka fi noman Dawa, Gero da sauran.

A cikin Bauchi ta kudu, sun fi yin noman masara da kuma shinkafa, hakan ya biyu bayan yallawattaccen ruwan saman da Allah ke azurta su da shi ne a kowace shekara. A yayin da su kuma Bauchi ta Arewa yanayinsu bai ba su damar samun wannan ribar kamar kudu ba; sakamakon yanayin muhallin nasu.

Noma dai kamar yadda mu ka fara ambatawa a sama, sana’a ce wacce mutum zai yi domin kare rayuwarsa daga fadawa cikin kangin talaucin rayuwa, a bisa haka ne ma’aikatan gwamnati musamman wadanda suka yi ritaya sukan rungumi sana’ar domin tallafa wa rayuwarsu bayan kammala aikinsu na gwamnati. Ga dukkaninin wani ma’aikacin gwamnati da ke da wayo zai rungumi Noma a matsayin makamin rayuwarsa.

Kai ba ma ma’aikacin gwamnati ba, ga dan kasuwa ko wanda bai da sana’ar yi, noma sana’ace saukakakkiya wacce zata baiwa mutum damar ciyar da rayuwarsa gaba ba tare da dogaro da wani ba.

A bisa haka ne na samu zantawa da wani fitaccen manomi a jihar Bauchi Alhaji Abdullahi Baba Akuyam (Sarkin Yakin Misau) wanda ya jima sama da shekaru yana sana’ar Noma, ya fara sana’arta ta noma tun yana karamin ma’aikacin gwamnati a shekara ta 1967 har ya zo yayi ritaya a shekara ta 2005. ya yi ritaya a aikin gwamnati shekaru 12 da suka gabata daga bisani ya rungumi sana’ar noma gabaki daya a rayuwarsa wanda yanzu haka yake ci da sha da sana’ar noma. yanzu haka da sana’ar noma yake ciyar da iyalansa sama da ashirin da matasan da kuma kyautata wa ‘yan uwa musamman makwafta “Ni a halin yanzu akwai wadanda suke karkashina da daman gaske wanda da wannan sana’ar noman na ke daukan dawainiyarsu, ga kuma ‘ya’yana 10 da jikiki dukka da wannan sana’ar noman na ke daukan dawainiyarsu na karatu, abinci, harkokin yau da kullum dukka da sana’ar noma.

Kai uwa-uba akwai jama’ar Annabi idan na fito da amfanin gona to ba ni kadai na ke ci ba, nakan raba ga makwaitana da kuma wadanda suke kusa. Duk wani manoma yakan so yayi noma ya yi kyauta da sadaka haka nima na ke. da zarar amfanin gonata ya fito nakan dauki amfanin na raba ga jama’a na kuma samu wanda zai dauke min nauyin da ke kaina dukka a sakamakon sana’ar noman da na yi. Ka ga wannan babbar nasarace sosai, kuma daidai gwargwado rayuwata tana kyautatu da wannan sana’ar ta noma. yau da a ce lokacin da na yi ritaya na zo na zauna haka nan zan samu wannan damar?”. In ji shi a lokacin da ke min bayani kan nasarar da ke samu a sha’anin Noma.

Abdullahi Baba Akuyam wanda har ila yau shi ne shugaban masu noman masara a jihar Bauchi (MAN) ya ci gaba da min bahasi kan sana’ar noma “Ni na kasance manomi tun ina aikin gwamnati, tun ina amsar rance ana cirewa a cikin albashina har na zo na kammala aikin gwamnati sai na dawo na maida hankali kwaco-kam akan noma, yanzu haka bana da wani sana’a ko wani abun yi da ta wuce noma.

“Abun da kuma na fi nomawa ita ce masara, ina kuma noma gyada, wake, waken suya, na taba yin noman ridi amma gaskiya bai amsheni ba. Sannan a jihar Bauchi manomanmu sun fi noman masara a ta nan kudancin Bauchi, sannan a kudancin kuma ana noman shinkafa sosai amma bata kai na masara ba. kudancin Bauchi irin garuruwan Darazau, Ganjuwa, cikin Bauchi, Alkaleri, Tafawa Balewa, Bogoro, Dass, Toro, da kuma Ningi duk sun fi karfi wajen noman masara wasu sukan hada da shinkafa da sauransu. Amma dai wadannan yankin na kudancin Bauchi Masara itace ja gaban nomarmu”.

Ya ci gaba da sahalewa “Su kuma Arewacin Bauchi Irin su Misau, Damban, Zaki, Itas Gadau, Shira su wadannan sun fi yin noman Dawa, Gero da kuma Gyada. Allah ya yi musu alamnashara domin dukkanin kogunan Bauchi sukan je ta can su tare ne hakan ke basu damar shuka Alkama da shinkafa a ta can arewacin Bauchi”. In ji shi

Da yake mana bayani kan ribar da ke cikin noman “Gaskiya ni ina shaida maka banga abun da ke da riba irin noma ba; shiyasa a duk inda na samu dama na ke kira ga jama’a kowace irin sana’a kake yi ka rungumi noma, idan ma ba zaka maida noman sana’arka ba to ka ke dan ware masa wani lokaci kana yinsa domin ribar da ke ciki. idan kai dan kasuwa ne ko ma’aikacin gwamnati a kalla in dai kai magidanci ne ka yi kokari ka noma akalla hekta daya, idan ka samu dama ka yi hekta biyu, wannan zai isheka abincin shekara guda.

“Tabbas dan kasuwa, makiyayi da ma’aikatan gwamnati su daure suke dan taba nomar nan akwai alfanu sosai a cikinsa. Ka ga ni babu wani abun da a yanzu bada noma na ke tafiyar da shi ba a cikin rayuwata”.

Baba Akuyam wanda a duk shekara akalla yake girban buhun masara sama da 150, ya kan kuma fitar da gyada, da su waken suya duk shekara kusan 150 wasu lokutan ma fiye.

Abdullahi Baba Akuyam ya ce yanzu haka suna samun ci gaba ta fuskacin samun Takin Noma sosai a bisa haka ya ce wannan babbar nasarace wajen rage tsadar rayuwa da al’umman Nijeriya da ke fama da su “Gaskiya tun da na ke noma shekaru da dama, bamu taba samun taimako mu manoma taimakon da muka ji ya shiga jikinmu irin na daminar bana ba; domin a da muna kokawa kan cewar taki bata isowa hanun mu manoma.

“Amma a yanzu ita gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Bauchi sun yi matukar kokari wajen ganin taki ya iso ga talakawa manoma. Dalili kuwa an rage farashin taki yanda kowa zai iya saya. Lokacin da aka rage farashin taki bana ma kasar nan amma da na dawo na ji yanda aka rage taki ya yi arha kuma ana samunsa a kasuwa wanda bai wuce dubu biyar da dari biyar ba; wannan rage kudin ya taimaka wa manoma sosai, da kuma samunsa da ake yi a kasuwa, da ga tsada kuma ba zaka samu ba ma. Taki ya wadaci manoma sosai a jihar Bauchi, kuma lallai babu kukan taki domin ana samun nasara sosai wajen ci gaban noma a jihar Bauchi”.

Da yake magana kan ‘yan uwansa ‘yan ritaya kuma ya ce bai dace ma’aikacin gwamnati ya tsaya zura ido ba tare da ya yi wa kansa tanadin barin aiki don fuskantar rayuwa ta gaba “Idan ma’aikaci bai yi wa kansa tanadin rayuwa ta gaba ba akwai matsala, kada ka tsaya cewa noma da wuya ko babu taki ko makamancin haka, da taki buhu biyu zaka iya noma, ita noma ba na mai kudi bane, na mai son yi ne mai neman sana’ar dogaro da kai, ina sake nanatawa tabbas noma ba na mai kudi bane, da taki buhu 2 ka nemi irin noma mudu biyu na masa ko na shinkafa zaka yi nomarka”. A cewarsa

Baba Akuyam ya kalubalanci matasan Nijeriya da suke ta kukan babu aikin yi a Nijeriya da cewa sune dai basu ga damar nemna aikin yi ba, domin noma sana’ace wacce matasa ya kamata su rungumeta a halin yanzu domin yanzu zamani ne na neman na kai, daga bisani sai ya nemi gwamnati ta ke karfafan matasa kan noma da tallafa musu da kayyakin noman domin su ma a dama da su, ya hakikance kan cewar da zarar matasa suka rungumi noma tabbas za a fita daga kuncin rayuwa.

Da yake magana kan leburori masu ci da sha a kan noman ya ce “yanzu leburori suna tsauwala kudin aikin da suke yi wa manoma sosai, idan suka tsauwala ka fito da amfanin goma zuwa kasuwa ka ga dole ta yi tsada”. In ji shi

To ko manoma suna da wani bukata domin gwamnati ta tallafa musu sai ya kada baki ya ce “Da bukatar gwamnati ta samar wa manoma kayan aiki irin su tirakta, garma, a kuma baiwa talakawa bashin noma, a kuma tabbatar wadanda za a basu bashin manoman ne. idan gwamnati ta samar wa manoma kayan aiki wahalar tsadar leburori zai yi sauki domin ga kayan aiki a kasa.

“Sannan kuma wata riba a kan riba shi noma ba fa ya kagewa, amma danyen Mai na iya kagewa ko ya yi tsada, don haka ina kira ga gwamnati ta fi maida hankali kan noma sosai fiye da sauran abubuwan domin mu fita daga damuwar talauci”. In ji masani a harkar ta noma

Wakilinmu ya labarta mana cewar yanzu haka gunakai masara a garuruwa mabanbata a jihar Bauchi sai hamdala, domin ko ta ina mutum ya bi zai tarar da noma ya yi albarka inda ake samun ci gaban masu yin noma sosai fiye da shekarun baya. Haka kuma an samu karin masu sha’awar noma ta fuskacin neman na kai.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Sirrin Iyayen Giji… MATA SAI DA ADO

Next Post

TARIHI: Tarihin Andaluz: Tsohuwar Daular Musulunci Da Ta Wanzu A Spain

RelatedPosts

Tarbiyyar ‘Ya Mace A Zamanance

Tarbiyyar ‘Ya Mace A Zamanance

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Daga A'isha Muhammad A wanna Mukalar zan yi duba ne...

Lokaci

Muhimmiyar Tsaraba Ga Ma’auratan Jiya Da Na Yau

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Daga Yusuf Kabir Aure yana daya daga cikin abin da...

Maleriya

Yaushe Za A Samar Da Riga-kafin Maleriya A Nijeriya?

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Najeeb Maigatari, A rubutun da ya gabata na dan...

Next Post

TARIHI: Tarihin Andaluz: Tsohuwar Daular Musulunci Da Ta Wanzu A Spain

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version