Umar A Hunkuyi" />

Mu Lazumci Shuka ‘Ya’yan Itatuwa Domin Sadaka Ce Mai Gudana – Kyaftin Umar

Tsaro ya na da fuskoki daban-daban; kula da lafiya, kula da tsafta, kula da muhalli duk su na cikin ma’anar tsaro. Siyasa ta na cikin tsaro, domin iDAn siyasa ba ta yi kyau ba, bakidayan harkoki sai su lalace, kasuwanci da sana’a duk su na cikin tsaro, domin rashin abin yi ya na iya kawo matsalar tsaro, rashin kulawa da harkar sufuri, ababen hawa, hanyoyi duk suna iya kawo matsalar tsaro.

Wadannan bayanan su na fitowa ne daga bakin Nebi Kyaftin Umar Abubakar mai ritaya a lokacin da ya ke yi wa al’umma tanbihi a kan faidar yin shuke-shuke, musamman shuka ‘ya’yan itatuwa masu yin ‘ya’yan marmari.

Kaftin Umar ya ci gaba da cewa: “A kan hakan ne na dubi abin da ya shafi shukawa ko dasa itatuwa. Da farko Musulunci ya nuna fa’idar hakan, musamman itatuwa masu kawo kudi, wannan sadaka ce mai gudana tsawon lokaci. Kadan daga cikin alfanun shukawa ko dasa ‘ya’yan itatuwa shi ne za su tsare mana shigowar Hamada, za su rage mana yawan kurar da ke damun jama’a, itatuwa a tsakaninmu suna shakan mugunyar iskar da muke fitarwa, su kuma suna fitar mana da kyakkyawar iskar da za mu shaka mu ni’imta mu kara lafiya. Shukawa ko dasa itatuwa a tsakanin mu yana rage mana zafin yanayi, duk inda ake dumaman yanayi na zafin da ya wuce kima, za ka ga ba su da itatuwa. Tsuntsaye kuma da kake ganin su a waje, alama ce ta zaman lafiya, duk inda ake zaman lafiya za ka samu tsuntsaye, amma duk inda ba a azaman lafiya ake talauci da rashin abinci za ka ga babu tsuntsaye a wajen. A dan zamanin baya a nan arewa da muke zaune lafiya, za ka ga muna da tsuntsaye masu yawa kala daban-daban, da sanyin safiya za ka ga Belbelu masu yawa sun fito za su tafi kiwon su, Jemagu, Tsadda, Kurciya ga su nan birjik duk inda ka duba za ka gansu , hatta Angulaye, a yanzun ko kwata ka je ba ka ganin Angulu. Domin a yanzun ne ba ma zaune lafiya, yanzun ne muke cikin talauci.

A zamanin baya babu gidan da suke yin abincin da zai ishe su su kadai, sai an yi da rara saboda almajirai za su zo. A lokacin da muke shuka itatuwan nan musamman masu fitar da ‘ya’yan marmari, za ka ga tsuntsayen nan sun zo suna sha, wanda wannan ma sadaka ne. Za kuma ka debi ‘ya’yan itatuwan nan ka siyar, wanda a nan ma ka kara samun kudin shiga ne. Don haka a nan, muke kira da babbar murya da cewa, misali in ka sha Mangwaro ka ajiye kwallon, ba wai Mangwaro kadai ba, duk wani dan itaciya da ka sha ka ji dadi sai ka ajiye kwallon, ka shanya su in ka fita daji, ko ka haka rami ka ajiye abinka ka yi tafiyarka musamman a wuraren watan Afrilu gab da za a fara ruwan sama, a nan ba sai an ba su ruwa ba, ka haka rami kawai ka zuba ko ka watsar da su, da Yardan Allah wasu daga cikin su za su fito. In ka dubi yawan mu misali a nan arewa, in a ce duk za mu yi hakan, ba karamar fa’ida ce za a samu ba.

Yanzun misali a nan Kaduna, ana ta rusa wurare domin ayyukan ci gaba, ana kuma biyan mutane hakkokin su, sai ka taras da wani babban gida an biya shi kimar kudin da bai kai ta wani karamin gidan ba, karamin gidan nan saboda suna da shukan itatuwa ne a cikin shi. Don haka, shuka itatuwa a gonakin mu, a gidajen mu, a hanyoyin mu da duk wuraren mu, hakan yana kara mana kima ne, zaman lafiya da wadatar lafiyan a jikkunan mu da muhallin mu. Ga kuma lada a wajen Allah da za mu ci gaba da samu har a bayan mutuwar mu, domin ka bar sadaka ce mai gudana.

In ka dubi Anguwannin a baya za ka ga duk ana sanya masu sunayen itatuwa kamar, ‘Yar’aduwa, Cediya biyu, Mangwaron dan Waire, Rimin Tsiwa, dan Marke, Mai Aduwa, ga su nan birjik, wanda duk wadannan sunayen itatuwa ne da Kakanninmu suka shuka su, amma mu yanzun muna yanke itatuwan nan muna yin girki da su alhalin ba wasu muke sake shukawa ba, ka ga kenan za a kai lokacin da babu itacen da za a yanke, amma idan da har muna shukawan ai ka ga da sauki, an cire daya an shuka goma. Yanda muke alfahari da jin dadin iyayen mu sun shuka mana, kai ma sai ka shuka wa ‘ya’yanka.

Sannan ganyayyakin itatuwan in suka zuba a kasa suka rube suna karawa kasa daraja a wajen noma domin su kansu taki ne, in ana ruwa ko zafin rana wasu a gindin itatuwa suke zuwa su fake, tsawa in ta zo a maimakon ta fadawa gida sai ta fadawa itace. To ka ga duk wadannan abubuwan da suke da alaka da shuka itatuwan taimaka wa kasar mu ce kuma taimakawa kawukanmu ne, sannan shuka itatuwan yana rage zaizayar kasa. In kuma ka duba, ba wani abu ne bambancin Anguwannin da ake cewa GRA da sauran Anguwannin mu ba face shuke-shuke. In ka shiga GRA za ka taras ga Fulawowi nan da sauran shuke-shuke duk an tsara su abin gwanin sha’awa, wanda idan da za mu yi shuke-shuken a ko’ina, sai ko’ina ma ya koma GRA din. Shi ya sanya a yanzun in ka je ka ajiye motarka ta kwana a GRA, da safe za ka taras da kura kadan ne a jikinta, amma in ka je wajen da babu itatuwan ka ajiye ta, ta ma yini, sai ka taras duk ta yi butu-butu kamar ba a gari daya ba.

Saboda haka, yana da matukar mahimmanci mu lizimci shuka itatuwa, a cikin garuruwan mu da kuma dazukan mu, musamman a yanda Allah Ya albarkace mu da kasa mai kyau a wannan kasar tamu, domin kusan za ka iya shuka kowane irin dan itace ya kuma fito ya yi daraja. Misali in ka je kasashen Asiya, suna da matsalar yanayin kasa sosai, amma kuma suna kokarin shuka itatuwa, domin a can in ka shuka itace to sai kuma ka sanya mashi fentin da zai hana gara ta cinye shi. Amma mu a nan ka sha mangwaro ka jefar kawai zai fito abin shi, in ma ka shiga dazukan mu ka ga itatuwa ka san wadannan ba shuka su ne aka yi ba, sun fito ne kawai. Amma da zaran ka je misali kasashen Asiya, da ganin itatuwan ga su nan a jere reras ka san wadannan shuka su ne aka yi aka kuma rene su.

Mu a nan a baya Sarakunan mu sun yi kokari matuka wajen shuka gandun daji, musamman Sarkin Katsina, Sir Usman Nagogo, inda ya yi umurni da kowane gari su shuka itace, shi ya sanya idan kana bin kauyakun Jihar Katsina, kana shiga cikin garin za ka ga itatuwa a jere a layi, amma a yanzun duk mun daina yin wannan. Amma muna kuma jin dadin abin da aka yi mana din na baya, shi ya sanya a nan nake jawo hankalin mutanan mu, wannan abin mu dawo da shi, duk wani dan itacen da muka sha, mu ajiye dan na shi mu bari su bushe, bayan sun bushe daga yanzun zuwa watan Afrilu lokacin da za a fara ruwan sama sai mu je mu shuka su a dazuka da sauran wurare, ba lallai sai gidanka ba ko ma wajen da ka sani, a duk inda ka zubar da su ko ka shuka su suka fito mutum ko dabba ko tsuntsu suka amfana da su ka sami ladan sadaka ne mai gudana.

Exit mobile version