Abubakar Abba" />

Mu Na Bukatar Tallafi Daga Gwamnatin Tarayya, Cewar Mata Manoma

Mata Manoma

Shugabar kungiyar mata kananan manoman Nijeriya, Mary Afan, ta bayyana cewa, sun bukaci gwamnatin tarayya ta dinga kwatan da sauran maza manoma yan uwan su wajen samar masu da inganataccen Irin noma, takin zamani da sauran kayan aikin noma.

Mary Afan ce ta sanar da hakan a cikin sanarwar da ta fitar, inda kuma ta yi nuni da cewa, matan kananan manoma a kasar nan sun kai a kalla kashi 72 bisa dari a kasar nan amma kuma basa samun tallafin aikin noma kamar yadda ya dace.

Idan za a iya tunawa, ganin irin mahimmancin da matan moman suke dashi ne a kasar nan, ya sa gwamnatin tarayya a kwanan baya ta kaddamar da tsarin bunkasa aikin noma na mata a kasar nan.

Shugabar kungiyar ta kasa Mary Afan ta kara da cewa, kungiyar tana da yayanta da su ka kai sama da 500,000 a karkara, inda kuma suka watsu zuwa zuwa cikin jihohi 36 na kasar nan harda Abuja.

A cewar Shugabar kungiyar ta kasa Mary Afan, duk da kashi 72 a cikin dari na matan kananan manoman da ake da su a kasar nan, an barsu a baya wajen samar masu da ingantaccen Irin noma, kayan aiki da sauran su.

Sai dai, Shugabar kungiyar ta kasa Mary Afan, kungiyar ta tura bukatar ta zuwa ga gwamnatin tarayya ta hanyar ma’aikatar aikin gona a raya karkara tare da yin hadaka da ma’aikatar walwalar mata ta tarayya don a samar ma su da ingataccen Irin noma, kayan aikin noma, takin zamani da sauransu.

Shugabar kungiyar ta kasa Mary Afan ta sanar da cewa, sakamakon samar da tsarin magance ban-bancin dake a a tsakanin mata manoma kanana da sauran maza manoma yan uwansu, a yau an iya samar da mata kanan manoma su 379,172 wadanda kuma aka hada su a a karkashin kungiyiyin guda 37,000 da ke a shiyoyi shida na kasar nan.

A cewar Shugabar kungiyar ta kasa Mary Afan, hakan ya bai wa kungiyar kwarin gwaiwar tura bukatar su zuwa ga gwamnatin tarayya ta hanyar ma’aikatar aikin gona da raya karkara tare da yin hadaka da ma’aikatar jin dadi da walwalar mata don a samarwa da matan kananan manoma takin zamani, inganatccen irin noma da kuma sauran kayan aikin gona.

Shugabar kungiyar ta kasa Mary Afan ta bayyana cewa, yawan dogaro kan amsu aikin a gona yana kara janyo gazawar samar da wadacaccen amnafin gona, inda kuma hakan yake ci gaba da kara janyo talauci a tsakanin mata kananan maoma da ke a fadin kasar nan.

A cewar Shugabar kungiyar ta kasa Mary Afan, matan manoma a kasar nan suna kuma fuskantar kalubale da dama da su ka hada da tafiyar da gidajen su da kuma lamain yanayin rashin tsaro, inda hakan ya ke hana masu zuwa gonakan su don yin noma.

Shugabar kungiyar ta kasa Mary Afan ina suka samu tallafin da ya dace, za su inya noma amfanin gonad a zai iya wadatar yan kasar nan har kuma a fitar dashi zuwa kasuwannin duniya don sayarwa.

Exit mobile version