Abubakar Abba">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NOMA

Mu Na Ganin Alfanun Shirye-shiryen Aikin Noma Na Gwamnatin Tarayya – Masu Ruwa Da Tsaki

by Abubakar Abba
January 5, 2021
in NOMA
2 min read
Musa Malumfashi

PIC.1. FARMERS WORKING ON A RICE FARM IN ZUMBA, NIGER STATE ON SUNDAY (11/9/11).

WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A cikin rahoton zango na hudu na shekarar 2019, da Hukumar Kididdiga tta Kasa (NBS) ta fitar a kwanan baya, ta ce, tattakin arzikin Nijeriya ya karu da kashi 2.3 a cikin dari a cikin shekarar idan aka kwatanta da kashi 1.9 a cikin dari a ahekarar 2018, inda tattalin arzikin kuma ya karu daga zwa kashi 2.55 daga shekara zuwa shekara.

Bugu da kari, a bisa wasu alkaluma da suka fito a kwanan baya daga gun Hukumomin Bloomberg da kuma Asusun bayar da lamuni na duniya IMF su ka fitar sun dira karfin tattalin arzikin Nijeriya kan mizanin mai karfin tattalin arziki a Afirka, inda kuma tattalin arzikin kasar, ya kai yawan dala biliyan 476, sai kuma tattalin arzikin kasar Afirka ta Kudu da ke bin na Nijeriya a baya da ya kai yawan dala biliyan 352 a 2019.

samndaads

Duk da matsin tattalin arziki da Nijeriya ta tsunduma a ciki a 2016, tattalin arzikin Nijeriya ya ci gaba da tsallake siradi.

Masu ruwa da tsaki da dama, sun danganta hakan kan wasu shirye-shiryen ayyukan noma da Babban Bankin Njieriya ya kirkiro dasu, inda su ka kara da cewa, shirye-shiryen aikin noma kamar su na Anchor Borrowers, rufe iyakokin Nijriya na kan tudu, kakaba takunkumi wajen samar da kudaden musaya na kasar waje, kakaba takunkumin hana shigo da wasu kayan abinci daga waje da sauransu.

Shirin na Anchor Borrowers ya kara da cewa, har yanzu a ganinsa, shi ne ya fi kyau, musamman ganin yadda CBN ya rage kudin ruwa daga kashi 9 cikin dari zuwa kashi 5 a cikin dari.

Shi kuwa Dakta Samaila Aliyu ya yi nuni da cewa, inda an wanzar da ragin kudin ruwan da ka yi a kwanan baya, hakan bawai kawai zai kara fadada shirin na Anchor Borrowers, zai kuma samar da sauki wajen samun masu shiga fannin da dama.

Shi ma Shugaban kungiyar kafar aikin noma ta kasa NAP Dakta Ademola Adesina, a hirarsa ta wayar tarho da manema labarai ya ce, ragin zai taimaka wajen habaka fannin da kuma kara samar da riba ga wadanda su ke a cikin fannin tare da bunkasa tattalin arzikin kasar.

Shugaban kungiyar kafar aikin noma ta kasa NAP Dakta Ademola Adesina, ya kara da cewa, kalubalen da ake fuskanta a yanzu a fannin tattalin arziki a fadin duniya, ba wanda zai lanunci karin kudin ruwa, amma CBN ya dauki matakin ne don rage radadin annobar korona da ke ci gaba da narkar da tattakin arziki a fadin duniya.

Shi ma a nasa ra’ayin Shugaban kungiyar Masu Kiwon Kaji ta Kasa Mista Ezekiel Ibrahim a hirarsa da manema labarai a babban birinin tarayyar Abuja ya yi nuni da cewa, taimakon zai jima ya na yin amfani da fannin.

Shugaban kungiyar Masu Kiwon Kaji ta Kasa Mista Ezekiel Ibrahim a karshe ya nuna jin dadinsa kan kokarin da bankin na CBN ya yi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Dalilin Da Ya Sa Farashin Albasa Ya Fadi Warwas A Wasu Jihohi

Next Post

Yadda ’Yar Shekara 60 Ta Kada ’Yan Mata A Gasar Sarauniyar Kyau

RelatedPosts

Manoman Masara A Gombe Za Su Dara – Kwamishina 

Manoman Masara A Gombe Za Su Dara – Kwamishina 

by Abubakar Abba
7 hours ago
0

Kwamishinan Gona da Dabbobi na Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Magaji...

An Sharwaci Nijeriya Ta Rika Tattaunawa Da Masana’antun Madara Na Cikin Gida

An Sharwaci Nijeriya Ta Rika Tattaunawa Da Masana’antun Madara Na Cikin Gida

by Abubakar Abba
7 hours ago
0

Darakta Janar na kungiyar nan ta, wato NECA, Dakta Timothy...

Tanadin Abinci Yana Da Mahimmanci Ga Al’umman Nijeriya, Inji Ministan Noma

Akwai Wawaken Gibi A Bangaren Noman Zamani A Nijeriya, Cewar Nanono

by Abubakar Abba
7 hours ago
0

Ministan Ma’aikatar Aikin Noma da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono...

Next Post
Yadda ’Yar Shekara 60 Ta Kada ’Yan Mata A Gasar Sarauniyar Kyau

Yadda ’Yar Shekara 60 Ta Kada ’Yan Mata A Gasar Sarauniyar Kyau

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version