Abubakar Abba" />

Mu Na Sa Ran Noma Shinkafa Mai Yawa A Kaka – Andami

Shugaban kungiyar masu noman shinkafa ta kasa reshen jihar Taraba, Mallam Tanko Bobbo Andami ya yabawa Gwamnatin Tarayya kan bashin data baiwa wasu daga cikin manoman shinkfa da ke a a cikin jihar.

Mallam Tanko Bobbo Andami ya yi wannan yabon ne  hirarsa da manema labarai a jihar ta Taraba, inda ya yi nuni da cewa, bashin zai taimakwa manoman Shinkafar na jihar su dari da suka amfana da bashin tai taimakawa sana’ar tasu ta noma.
Yaci gaba da cewa, bashin wanda gwamnatin Tarrayya ta bayar da  lamuni ta karkashin babban bankin Nijeriya, watau CBN, an bayar da shi da nufin kara bunkasa noman shinkafa a Jihar.
A cewar Shugaban kungiyar masu noman shinkafa ta kasa reshen jihar Taraba, Mallam Tanko Bobbo Andami, gwamnatin Tarrayya ta, bullo da shirin baiwa manoman shinkafar bashin ne don ta basu goyon baya da  karfafa gwarin gwiwa don noma Shinkafa mai yawa da zata wataci kasar nan baki daya.
Malam Tanko Bobbo Andami ya kara da cewa, hakan zai kuma rage yawan shigo da shinkafa daga kasashen waje zuwa cikin kasar nan.
Ya ce, Taraba ta na daya daga cikin jihohin a cikin Nijeriya da ake moma shinkafa mai dimbin yawa shi, inda ya yi nuni da cewa, hakan ne baiwa Gwamnatin kwarin gwaiwa da kuma yin tunani don ta azawa manoman shinkafar dake jihar da bashin da kuma kayan aikin noma.
A cewar Malam Tanko Bobbo Andam Allah ya albarkaci jihar Taraba  da manyan koguna wadanda suka ratsa sassan Jihar daban daban, hakan ya baiwa manoman damar noma shinkafar rani da kuma a lokacin yanayi damina.
Shugaban ya sanar da cewa,  kayan noman sun hada injin ban ruwa, takin zamani, irin shinkafa da kuma maganin feshi na kashe ciyawa.
A cewar shugaban kungiyar, maniman da suka amfana da bashin,  zasu biya bashin ne idan sun girbe amfanin gonakan su.
Ya yi  nuni da cewa, sabanin a baya, inda aka rabawa mamonan bashi ba tare da sun ajiye komai ba amma a wannin likacin  an bullo da tsarin  sai an ga gonar dukkan manimin dake noma shinkafa  kafin su amafana da bashin.
Bugu da kari shugaban ya ce, moman da zasu amfana da bashin da kuma kayan noman,   ana bukatar su bayar da kashi 20 na yawan kudin bashin da za a basu a matsayin kudin ajiya.
Shugaban  Tanko Bobbo Andami ya ce  Maniman da suna amfana da   bashin zasu biya sau biyu ne, inda ya kara da cewa, wannan bashin ba kyauta ba ne,  a saboda haka kada maomi ya karba yaki maidowa ya dauka cewa yaci bulus wannan ba haka ba ne.

Exit mobile version